YouVersion Logo
Search Icon

Neh 12

12
Firistoci da Lawiyawa
1Firistoci da Lawiyawa da suka komo tare da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa, su ne
Seraiya, da Irmiya, da Ezra,
2-7Amariya, da Malluki, da Hattush,
Shekaniya, da Rehum, da Meremot,
Iddo, da Ginneton, da Abaija,
Miyamin, da Mawadiya, da Bilga,
Shemaiya, da Yoyarib, da Yedaiya,
Sallai, da Amok, da Halkiya, da Yedaiya.
Waɗannan su ne shugabannin firistoci da 'yan'uwansu a zamanin Yeshuwa.
8-9Lawiyawa su ne,
Yeshuwa, da Binnuyi, da Kadmiyel,
Sherebiya, da Yahuza, da Mattaniya wanda yake lura da waƙoƙin godiya, da shi da 'yan'uwansa.
Bukbukiya da Unno, 'yan'uwansu, suka tsaya daura da su a taron sujada.
Zuriyar Yeshuwa Firist
10Yeshuwa shi ne ya haifi Yoyakim, Yoyakim ya haifi Eliyashib, Eliyashib ya haifi Yoyada. 11Yoyada ya haifi Jonatan, Jonatan ya haifi Yadduwa.
Shugabannin Iyalin Firistoci
12-21A zamanin Yoyakim babban firist, waɗannan su ne shugabannin iyalin firistoci,
na wajen Seraiya, Meraiya ne
na wajen Irmiya, Hananiya ne
na wajen Ezra, Meshullam ne
na wajen Amariya, Yehohanan ne
na wajen Malluki, Jonatan ne
na wajen Shebaniya, Yusufu ne
na wajen Harim, Adana ne
na wajen Merayot, Helkai ne
na wajen Iddo, Zakariya ne
na wajen Ginneton, Meshullam ne
na wajen Abaija, Zikri ne
na wajen Miniyamin da Mowadiya, Filtai ne
na wajen Bilga, Shimeya ne
na wajen Shemaiya, Yehonatan ne
na wajen Yoyarib, Mattenai ne
na wajen Yedaiya, Uzzi ne
na wajen Sallai, Kallai ne
na wajen Amok, Eber ne
na wajen Hilkiya, Hashabiya ne
na wajen Yedaiya, Netanel ne.
Lissafin Manya na Iyalin Firistoci da Lawiyawa
22A zamanin Eliyashib, da Yoyada, da Yohenan, da Yadduwa, Lawiyawa, har zuwa zamanin mulkin Dariyus, mutumin Farisa, aka rubuta shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa da firistoci.
23Aka kuma rubuta shugabannin gidajen kakannin zuriyar Lawi a tarihi, har zuwa zamanin Yohenan ɗan Eliyashib.
An Rarraba Ayyukan Haikali
24Shugabannin Lawiyawa kuwa, su ne Hashabiya, da Sherebiya, da Yeshuwa, da Kadmiyel. 'Yan'uwansu suna tsaye kusa da su daki daki domin su yi yabo, su yi godiya kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.
25Mattaniya, da Bakbukiya, da Obadiya, da Meshullam, da Talmon, da Akkub su ne masu tsaron ƙofofi, suna tsaron ɗakunan ajiya na wajen ƙofofi.
26Waɗannan suna nan a zamanin Yoyakim ɗan Yeshuwa, jikan Yehozadak, da zamanin mai mulki Nehemiya, da Ezra, firist da magatakarda.
An Keɓe Garun Birni
27A lokacin keɓe garun Urushalima, sai aka nemo Lawiyawa a wurarensu duka don a kawo su Urushalima, su yi bikin keɓewa da farin ciki da godiya, da raira waƙoƙi da kuge, da garaya, da molo. 28Aka tattara mawaƙa daga kewayen Urushalima da ƙauyukan Netofatiyawa. 29Da kuma daga Betgilgal da karkarar Geba, da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima. 30Sai firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma tsarkake jama'a, da ƙofofi, da garun.
31Sai na sa shugabannin Yahuza su hawo garu, sa'an nan na sa manyan ƙungiyoyi biyu waɗanda za su yi godiya, su tafi a jere.
Ƙungiya guda ta bi wajen dama a kan garun zuwa Ƙofar Juji. 32Hoshaiya da rabin sugabannin Yahuza suka bi bayansu, 33tare da Azariya, da Ezra, da Meshullam, 34da Yahuza, da Biliyaminu, da Shemaiya, da Irmiya. 35Sa'an nan waɗansu 'ya'yan firistoci, masu busar ƙaho, su ne Zakariya ɗan Jonatan, jīkan Shemaiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, da Mikaiya, da Zakkur, daga zuriyar Asaf. 36Sauran 'yan'uwansa su ne Shemaiya, da Azarel, da Milalai, da Gilalai, da Ma'ai, da Netanel, da Yahuza, da Hanani. Suna da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗekaɗe. Ezra magatakarda ne yake gabansu. 37A Ƙofar Maɓuɓɓuga kuwa, sai suka yi gaba sosai wajen matakan birnin Dawuda, wajen hawan garu, daga bisa gidan Dawuda, zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas.
38Ƙungiyar jama'a ta biyu ta masu yin waƙoƙin godiya, ta bi ta wajen hagu. Na bi su tare da rabin jama'a a kan garu, sama da Hasumiyar Tanderu zuwa garu mai fādi, 39da Kuma sama da Ƙofar, Ifraimu da wajen Tsohuwar Ƙofar, da wajen Ƙofar Kifi, da Hasumiyar Hananel, da Hasumiyar Ɗari zuwa Ƙofar Tumaki, sai suka tsaya a Ƙofar Tsaro.
40Haka fa ƙungiyoyi biyu ɗin nan masu raira waƙoƙin godiya suka tsaya a Haikalin Allah.
Ni da rabin shugabanni muna tare da su. 41Tare da firistoci kuma, wato su Eliyakim, da Ma'aseya, da Miniyamin, da Mikaiya, da Eliyehoyenai, da Zakariya, da Hananiya, suna busa ƙaho, 42da kuma Ma'aseya, da Shemaiya, da Ele'azara, da Uzzi, da Yehohanan, da Malkiya, da Elam, da Ezer, suna raira waƙoƙi, Yezrahiya kuma shi ne shugabansu. 43Jama'a suka miƙa hadayu da yawa a wannan rana, suka yi murna, gama Allah ya faranta musu zuciya ƙwarai. Mata da yara kuma suka yi murna. Aka ji muryar murnar mutanen Urushalima daga nesa.
Shiri don Firistoci da Lawiyawa
44A ran nan aka sa mutanen da za su lura da ɗakunan ajiya, da sadakoki, da nunan fari, da zaka. Su ne za su tara nunan fari daga gonakin da suke kusa da garuruwa, bisa ga yadda doka ta ce, saboda firistoci da Lawiyawa, gama mutanen Yahuza sun yi murna saboda hidimar da firistoci da Lawiyawa suka yi. 45#1Tar 25.1-8; 1Tar 26.12 Sun yi wa Allahnsu sujada, sun yi hidimar tsarkakewa tare da mawaƙa da masu tsaron ƙofofi kamar yadda Dawuda da ɗansa Sulemanu suka umarta. 46A dā a zamanin Dawuda da Asaf akwai shugaban mawaƙa, akwai kuma waƙoƙin yabo da na godiya ga Allah. 47A zamanin Zarubabel da zamanin Nehemiya dukan jama'ar Isra'ila suka biya wa mawaƙa da masu tsaron ƙofofi bukatarsu ta kowace rana. Sun kuma ba Lawiyawa sadokoki, su Lawiyawa kuma suka ba zuriyar Haruna nasu rabo.

Currently Selected:

Neh 12: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy