YouVersion Logo
Search Icon

Mak 5

5
Addu'ar Neman Jinƙai
1Ya Ubangiji, ka tuna da abin da ya same mu.
Ka duba, ka ga yadda muka zama abin kunya!
2An ba baƙi gādonmu,
Gidajenmu kuwa an ba bare.
3Mun zama marayu, marasa ubanni,
Uwayenmu sun zama kamar matan da mazajensu sun mutu.
4Dole ne mu biya ruwan da za mu sha,
Dole ne kuma mu sayi itace.
5Masu binmu a ƙyeyarmu suke, suna korarmu da zafi,
Mun gaji, ba a yarda mu huta.
6Mun miƙa hannu ga Masar da Assuriya
Don mu sami abinci.
7Ubanninmu sun yi zunubi, ga shi kuwa, ba su,
Mu kuwa muna ɗaukar alhakin muguntarsu.
8Bayi suke mulkinmu,
Ba kuwa wanda zai cece mu daga hannunsu.
9Sai mun yi kasai da ranmu kafin mu sami abinci,
Domin akwai masu kisa a jeji.
10Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu,
Saboda tsananin yunwa.
11An yi wa mata faɗe a cikin Sihiyona,
Haka kuma aka yi wa budurwai a garuruwan Yahuza.
12An rataye shugabanni da hannuwansu,
Ba a kuma girmama dattawa ba.
13An tilasta wa samari su yi niƙa,
Yara kuma suna tagataga da kayan itace.
14Tsofaffi sun daina zama a dandalin ƙofar birni,
Samari kuma sun daina bushe-bushe.
15Farin cikinmu ya ƙare,
Raye-rayenmu sun zama makoki.
16Rawani ya fāɗi daga kanmu,
Tamu tu ƙare, gama mun yi zunubi!
17Saboda wannan zuciyarmu ta ɓaci,
Idanunmu kuma suka duhunta.
18Gama Dutsen Sihiyona ya zama kufai,
Wurin yawon diloli.
19Amma ya Ubangiji, kai ne kake mulki har abada,
Kursiyinka ya dawwama har dukan zamanai.
20Don me ka manta da mu har abada?
Don me ka yashe mu da daɗewa haka?
21Ya Ubangiji, ka komo da mu zuwa gare ka!
Mu kuwa za mu koma.
Ka sabunta kwanakinmu su zama kamar na dā.
22Ko ka ƙi mu ne, sam sam?
Ko kuwa ka husata da mu?

Currently Selected:

Mak 5: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in