Mak 4
4
Bayan Faɗuwar Urushalima
1Ƙaƙa zinariya ta zama duhu!
Ƙaƙa zinariya tsantsa ta sāke!
Tsarkakakkun duwatsu kuma suna zube
A kowane magamin titi.
2Darajar samarin Sihiyona
Ta kai tamanin zinariya tsantsa.
To, ƙaƙa ake lissafinsu kamar tukwanen ƙasa,
Aikin hannun maginin tukwane?
3Ko diloli ma sukan ba 'ya'yansu mama,
Su shayar da su.
Amma mutanena sun zama kamar jiminai cikin jeji.
4Harshen jinjiri ya liƙe a dasashinsa saboda ƙishi,
'Yan yara suna roƙon abinci,
Amma ba wanda ya ba su.
5Su waɗanda suka ci abubuwa masu daɗi,
Sun halaka a titi.
Su waɗanda aka goye su da alharini,
Yanzu suna kwance a kan tsibin toka.
6 #
Far 19.24
Gama zunubin mutanena
Ya fi zunubin Saduma,
Wadda Ubangiji ya hallakar da ita nan da nan.
7Keɓaɓɓunta sun fi dusar ƙanƙara tsabta,
Sun kuma fi madara fari.
Jikunansu sun fi murjani ja.
Kyan tsarinsu yana kama da shuɗin yakutu.
8Yanzu fuskokinsu sun fi kukunniya baƙi,
Ba a iya fisshe su a titi ba,
Fatar jikinsu ta liƙe wa ƙasusuwansu,
Sun bushe kamar itace.
9Gara ma waɗanda takobi ya kashe
Da waɗanda yunwa ta kashe,
Gama sun rame sarai saboda rashin abinci.
10 #
M.Sh 28.57; Eze 5.10 Mata masu juyayi, da hannuwansu
Suka ɗauki 'ya'yansu, suka dafa,
Suka zama musu abinci a lokacin halakar mutanena.
11Ubangiji ya saki fushinsa,
Ya zuba fushinsa mai zafi.
Ya kunna wa Sihiyona wuta
Wadda ta cinye harsashin gininta.
12Sarakunan duniya da mazaunanta ba su gaskata,
Cewa abokan gaba ko maƙiya
Za su iya shiga ƙofofin Urushalima ba.
13Dalili kuwa saboda zunuban annabawa ne,
Da muguntar firistoci,
Waɗanda suka kashe adalai.
14Sun yi ta kai da kawowa a titi kamar makafi,
Sun ƙazantu da jini
Har ba wanda zai taɓa rigunansu.
15Mutane suka yi ta yi musu ihu,
Suna cewa, “Ku tafi, ku ƙazamai,
Ku tafi, ku tafi, kada ku taɓa mu!”
Don haka suka zama korarru, masu kai da kawowa.
A cikin sauran al'umma mutane suna cewa,
“Ba za su ƙara zama tare da mu ba.”
16Ubangiji kansa ya watsar da su,
Ba zai ƙara kulawa da su ba.
Ba su darajanta firistoci ba,
Ba su kuma kula da dattawa ba.
17Idanunmu sun gaji
Da zuba ido a banza don samun taimako,
Mun zuba ido
Ga al'ummar da ba za ta iya cetonmu ba.
18Ana bin sawayenmu,
Don haka ba mu iya tafiya a titunanmu ba.
Ƙarshenmu ya yi kusa,
Kwanakinmu sun ƙare,
Gama ƙarshenmu ya zo.
19Masu runtumarmu sun fi gaggafar da take tashi sama sauri.
Sun fafare mu a kan duwatsu,
Suna fakonmu a cikin jeji.
20Shi wanda muke dogara gare shi,
Wato zaɓaɓɓe na Ubangiji, ya auka cikin raminsu,
Shi wanda muka ce,
“A ƙarƙashin inuwarsa ne za mu zauna a cikin sauran al'umma.”
21Ki yi farin ciki, ki yi murna, ke Edom,
Wadda kike zaune cikin ƙasar Uz.
Amma fa za a ba ki ƙoƙo ki sha,
Ki bugu har ki yi tsiraici.
22Ya Sihiyona, hukunci a kan muguntarki ya ƙare,
Ba zai ƙara barinki a ƙasar bauta ba.
Amma zai hukunta ki saboda muguntarki, ya Edom,
Zai tone zunubanki.
Currently Selected:
Mak 4: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979