Mak 3
3
Sa Zuciya ga Samun Taimako daga Wurin Ubangiji
1Ni ne mutumin da ya sha wuyar horon Ubangiji.
2Ya kore ni zuwa cikin duhu baƙi ƙirin.
3Hakika ikonsa ya yi ta gāba da ni dukan yini.
4Ya sa naman jikina da fatar jikina su lalace,
Ya kuma kakkarya ƙasusuwana.
5Ya kewaye ni da yaƙi,
Ya rufe ni da baƙin ciki mai tsanani da wahala.
6Ya zaunar da ni cikin duhu,
Kamar waɗanda suka daɗe da mutuwa.
7Ya kewaye ni da garu don kada in tsere,
Ya ɗaure ni da sarƙa mai nauyi.
8Ko da yake ina kira, ina kukan neman taimako,
Ya yi watsi da addu'ata.
9Ya toshe hanyata da sassaƙaƙƙun duwatsu,
Ya karkatar da hanyoyina.
10Ya zamar mini kamar beyar wanda yake fako,
Kamar zaki a ɓoye cikin ruƙuƙi.
11Ya bauɗar da ni daga hanyata, ya yayyage ni,
Ya maishe ni, ba ni a kowa.
12Ya ja bakansa, ya sa in zama abin baratarsa.
13Ya harbe zuciyata da kiban kwarinsa.
14Na zama abin dariya ga dukan mutane,
Dukan yini suna yi mini waƙar zambo.
15Ya shayar da ni da ruwan ɗaci,
Ya ƙosar da ni da abinci mai ɗaci.
16Ya sa in tauna tsakuwa da haƙorana,
Ya zaunar da ni cikin ƙura.
17An raba ni da salama,
Na manta da abar da ake ce da ita wadata.
18Sai na ce, “Darajata ta ƙare,
Ba ni kuma da sa zuciya wurin Ubangiji.”
19Ka tuna da azabata, da galabaitata,
Da ɗacin raina, da kumallon da nake fama da shi.
20Kullum raina yana tunanin azabaina,
Raina kuwa ya karai.
21Da na tuna da wannan, sai na sa zuciya ga gaba.
22Ƙaunar Ubangiji ba ta ƙarewa,
Haka kuma jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
23Su sababbi ne kowace safiya,
Amincinka kuma mai girma ne.
24Na ce, “Ubangiji shi ne nawa,
Saboda haka zan sa zuciya gare shi.”
25Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke sauraronsa,
Da wanda suke nemansa kuma.
26Yana da kyau a jira ceton Ubangiji da natsuwa,
27Yana da kyau mutum ya hori kansa tun yana yaro.
28Bari ya zauna a kaɗaice, ya yi shiru
Sa'ad da yake da damuwa.
29Bari ya kwanta cikin ƙura,
Watakila akwai sauran sa zuciya.
30Bari ya yarda a mari kumatunsa,
Ya haƙura da cin mutunci.
31Gama Ubangiji ba zai yashe mu har abada ba.
32Ko da ya sa ɓacin rai,
Zai ji tausayi kuma,
Saboda tabbatacciyar ƙaunarsa mai yawa.
33Gama ba da gangan ba ne yakan wahalar da 'yan adam
Ko ya sa su baƙin ciki.
34Ubangiji bai yarda a danne
'Yan kurkuku na duniya ba.
35Bai kuma yarda a hana wa mutum hakkinsa
A gaban Maɗaukaki ba,
36Ko kuwa a karkatar wa mutum da shari'arsa.
37Wa ya umarta, abin kuwa ya faru,
In ba Ubangiji ne ya umarta ba?
38Ba daga bakin Maɗaukaki
Alheri da mugunta suke fitowa ne ba?
39Don me ɗan adam
Zai yi gunaguni a kan hukuncin zunubansa?
40Bari mu jarraba, mu bincika hanyoyinmu,
Sa'an nan mu komo wurin Ubangiji.
41Bari mu roƙi Allah na Sama,
Muna miƙa hannuwanmu sama, mu ce,
42“Mun yi zunubi, mun tayar,
Kai kuwa ba ka gafarta ba.
43“Ka yafa fushi, ka runtume mu,
Kana karkashe mu ba tausayi.
44Ka kuma rufe kanka da gajimare
Don kada addu'a ta kai wurinka.
45Ka maishe mu shara da juji a cikin mutane.
46“Dukan maƙiyanmu suna yi mana ba'a.
47Tsoro, da wushefe,
Da lalatarwa, da hallakarwa sun auka mana.
48Hawaye suna gangarawa daga idanuna kamar ruwan koguna,
Saboda an hallaka mutanena.
49“Hawayena suna ta gangarawa, ba tsayawa, ba hutawa,
50Har lokacin da Ubangiji daga Sama ya duba, ya gani.
51Ganin azabar 'yan matan birnina
Ya sa ni baƙin ciki.
52“Waɗanda suke maƙiyana ba dalili
Sun farauce ni kamar tsuntsu.
53Sun jefa ni da rai a cikin rami,
Suka rufe ni da duwatsu.
54Ruwa ya sha kaina,
Sai na ce, ‘Na halaka.’
55“Ya Ubangiji, na yi kira ga sunanka
Daga cikin rami mai zurfi.
56Ka kuwa ji muryata.
Kada ka rufe kunnenka ga jin kukana na neman taimako.
57Sa'ad da na yi kira gare ka, ka zo kusa.
Sa'an nan ka ce mini kada in ji tsoro.
58“Ka karɓi da'awata, ya Ubangiji,
Ka kuwa fanshi raina.
59Ka ga laifin da aka yi mini,
Sai ka shara'anta da'awata, ya Ubangiji.
60Ka ga dukan irin sakayyarsu,
Da dukan dabarun da suke yi mini.
61“Ya Ubangiji, ka ji zargi
Da dukan dabarun da suke yi mini.
62Leɓunan maƙiyana da tunaninsu
Suna gāba da ni dukan yini.
63Suna raira mini waƙar zambo sa'ad da suke zaune,
Da lokacin da suka tashi.
64“Ya Ubangiji, za ka sāka musu bisa ga ayyukansu,
65Za ka ba su tattaurar zuciya,
La'anarka kuwa za ta zauna a kansu!
66Da fushi za ka runtume su
Har ka hallaka su a duniya, ya Ubangiji!”
Currently Selected:
Mak 3: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979