Josh 4
4
Duwatsu Goma Sha Biyu da Aka Ɗauka Tsakiyar Urdun
1Da al'umma duka suka gama haye Urdun, sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa, 2“Ɗauki mutum goma sha biyu daga cikin jama'a, wato mutum ɗaya na kowace kabila. 3Ka umarce su su ɗauki duwatsu goma sha biyu daga tsakiyar Urdun daidai inda firistoci suka tsaya, su haye da su, su ajiye su a masaukin da za su kwana yau.” 4Sai Joshuwa ya kirawo mutum goma sha biyu waɗanda ya zaɓa daga cikin Isra'ilawa, mutum guda na kowace kabila.
5Ya ce musu, “Wuce gaban akwatin Ubangiji Allahnku zuwa tsakiyar Urdun, ko wannenku ya ɗauki dutse a kafaɗarsa, don kowace kabila ta Isra'ila. 6Wannan zai zama alama a gare ku, don ya yiwu wata rana 'ya'yanku za su tambaye ku, su ce, ‘Ina ma'anar waɗannan duwatsu a gare ku?’ 7Sa'an nan za ku faɗa musu cewa, ‘Domin an yanke ruwan Urdun a gaban akwatin alkawari na Ubangiji sa'ad da ya haye Urdun.’ Waɗannan duwatsu za su zama abin tunawa ga Isra'ilawa har abada.”
8Sai Isra'ilawa suka yi yadda Joshuwa ya umarta, suka ɗauki duwatsu goma sha biyu a tsakiyar Urdun bisa ga yawan kabilansu kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Joshuwa, suka haye da su zuwa inda suka sauka, a can suka ajiye su. 9Joshuwa kuma ya kafa duwatsu goma sha biyu a tsakiyar Urdun, a wurin da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suka tsaya, duwatsun suna nan har wa yau. 10Gama firistocin da suke ɗauke da akwatin sun tsaya a tsakiyar Urdun, har aka gama dukan abin da Ubangiji ya umarci Joshuwa ya faɗa wa jama'a, da kuma bisa ga dukan abin da Musa ya umarce shi.
Mutanen kuwa suka gaggauta, suka haye. 11Da jama'a duka suka gama hayewa, sai akwatin Ubangiji da firistocin suka wuce gaban jama'ar. 12Mutanen Ra'ubainu, da na Gad, da rabin kabilar Manassa kuwa suka haye tare da 'yan'uwansu da shirin yaƙi kamar yadda Musa ya umarce su. 13Mutum wajen dubu arba'in ne (40,000), mayaƙa, suka haye da shirin yaƙi a gaban Ubangiji zuwa filayen Yariko. 14A ranan nan Ubangiji ya ɗaukaka Joshuwa a idon dukan Isra'ilawa, har suka ga kwarjininsa dukan kwanakin ransa kamar yadda suka ga na Musa.
15Ubangiji kuma ya ce wa Joshuwa, 16“Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin shaida, su fito daga cikin Urdun.” 17Sai Joshuwa ya umarci firistocin su fito daga cikin Urdun. 18Da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka fito daga tsakiyar Urdun, suka taka sandararriyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya malalo ya tumbatsa kamar dā.
19Rana ta goma ga watan ɗaya jama'a suka haye Urdun, suka yi zango a Gilgal a gabashin iyakar Yariko. 20Joshuwa ya kafa duwatsun nan goma sha biyu da suka ɗauko daga Urdun a Gilgal. 21Sai ya ce wa Isra'ilawa, “Sa'ad da wata rana 'ya'yanku suka tambayi ubanninsu ma'anar duwatsun nan, 22sa'an nan za ku sanar da 'ya'yanku cewa Isra'ilawa sun haye Urdun da ƙafa a kan sandararriyar ƙasa! 23Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya ƙafe, har kuka haye kamar yadda Ubangiji Allahnku ya sa Bahar Maliya ta ƙafe har muka haye, 24domin dukan mutanen duniya su sani Ubangiji yana da iko, domin kuma ku kasance da tsoron Ubangiji Allahnku har abada.”
Currently Selected:
Josh 4: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979