Sai ya ce wa Isra'ilawa, “Sa'ad da wata rana 'ya'yanku suka tambayi ubanninsu ma'anar duwatsun nan, sa'an nan za ku sanar da 'ya'yanku cewa Isra'ilawa sun haye Urdun da ƙafa a kan sandararriyar ƙasa! Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya ƙafe, har kuka haye kamar yadda Ubangiji Allahnku ya sa Bahar Maliya ta ƙafe har muka haye