Josh 3
3
Isra'ilawa Sun Haye Urdun
1Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, da shi da dukan jama'ar Isra'ila, suka kama hanya daga Shittim zuwa Urdun, inda suka sauka kafin su haye. 2Bayan kwana uku sai shugabannin jama'a suka bibiya zango, 3suna umartar jama'ar suna cewa, “Sa'ad da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi, 4domin ku san hanyar da za ku bi, gama ba ku taɓa bin hanyar ba. Sai dai tsakaninku da shi za ku bar rata misalin nisan kamu dubu biyu, kada ku kusace shi.”
5Sai Joshuwa ya ce wa jama'a, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai aikata abin al'ajabi a tsakiyarku.” 6Ya kuma ce wa firistocin, “Ku ɗauki akwatin alkawari ku wuce gaban jama'ar.” Sai suka ɗauki akwatin alkawari suka wuce gaban jama'a.
7Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “A yau ɗin nan zan fara ɗaukaka ka a gaban dukan Isra'ilawa domin su sani, kamar yadda na kasance tare da Musa, haka kuwa zan kasance tare da kai. 8Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari cewa, ‘Sa'ad da kuka shiga gefen ruwan Urdun, sai ku tsaya cik a wurin.’ ”
9Joshuwa kuma ya ce wa Isra'ilawa, “Ku kusato ku ji zantuttukan Ubangiji Allahnku.” 10Joshuwa kuma ya ƙara da cewa, “Ta haka za ku sani Allah mai rai yana tsakiyarku, ba makawa kuwa zai kori Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Hiwiyawa, da Ferizziyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Yebusiyawa a gabanku. 11Ga shi, akwatin alkawari na Ubangijin dukkan duniya yana wucewa a gabanku zuwa cikin Urdun. 12Yanzu fa, ku ɗauki mutum goma sha biyu daga kabilanku, wato mutum ɗaya daga kowace kabila. 13A sa'ad da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangijin dukkan duniya, suka tsoma tafin sawunsu cikin ruwan Urdun, ruwan Urdun zai yanke, ruwan da yake gangarowa zai tsaya tsibi guda.”
14-15(Da kaka Urdun yakan yi cikowa makil.) Jama'a fa, suka tashi daga alfarwansu don su haye Urdun. Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suna gaba. Da firistocin suka tsoma ƙafafunsu cikin ruwa daga gefe, 16sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru wuri ɗaya, ya yi soro daga nesa kusa da Adam, birnin da yake kusa da Zaretan. Ruwan kuma da yake gangarowa zuwa Tekun Araba, wato Tekun Gishiri, aka yanke shi ɗungum. Jama'a kuwa suka haye daura da Yariko. 17A sa'ad da Isra'ilawa duka suna tafiya a kan sandararriyar ƙasa a cikin Urdun, firistoci kuwa waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka yi ta tsayawa a bisa sandararriyar ƙasa a tsakiyar Urdun har al'ummar ta gama hayewa.
Currently Selected:
Josh 3: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979