YouVersion Logo
Search Icon

Josh 18

18
Rarraba Ƙasa a Shilo
1Da jama'ar Isra'ila suka ci ƙasar, sai suka tattaru a Shilo inda suka kafa alfarwa ta sujada.
2Har yanzu akwai sauran kabila bakwai na Isra'ila waɗanda ba su sami gādonsu ba tukuna. 3Sai Joshuwa ya ce wa jama'ar Isra'ila, “Har yaushe za ku yi jinkirin shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku? 4Ku ba ni mutum uku daga kowace kabila, ni kuwa in aike su, su auna ƙasar yadda za a raba ta gādo, sa'an nan su komo wurina. 5Sai su raba ƙasar kashi bakwai. Kabilar Yahuza za ta ci gaba da zama a yankin ƙasarta a wajen kudu, mutanen gidan Yusufu kuwa su zauna a yankin ƙasarsu a wajen arewa. 6Ku auna ƙasar, ku raba ta kashi bakwai, sa'an nan ku kawo mini taswirar ƙasar. Ni kuwa zan jefa muku kuri'a a gaban Ubangiji Allahnmu. 7Lawiyawa ba su da rabo tare da ku gama aikin Ubangiji shi ne rabonsu, da rabin ta Manassa sun riga sun sami nasu rabo wanda Musa, bawan Ubangiji, ya ba su a hayin gabashin Urdun.”
8Joshuwa ya umarci mutanen da za su tafi su auna ƙasar, ya ce, “Ku shiga cikin ƙasar duka, ku auna sa'an nan ku komo wurina, ni kuwa zan jefa muku kuri'a a gaban Ubangiji a nan Shilo.” 9Sai mutanen suka tafi, suka ratsa ƙasar tudu da ta gangare, suka auna ƙasar, suka raba ta kashi bakwai, suka lasafta garuruwan da suke ciki, sa'an nan suka koma wurin Joshuwa a Shilo. 10Joshuwa kuwa ya jefa musu kuri'a a gaban Ubangiji a Shilo. Ta haka ya rarraba ƙasar ga jama'ar Isra'ila, kowa ya sami rabonsa.
Yankin Ƙasar da Aka Ba Biliyaminu
11Kuri'ar kabilar Biliyaminu bisa ga iyalanta ta fito. Yankin ƙasar da ya faɗo mata ke nan, ya zama a tsakanin yankin ƙasar kabilar Yahuza da na jama'ar Yusufu. 12A wajen arewa iyakar ta tashi daga Urdun, ta bi ta tsaunin da yake arewa da Yariko, ta kuma haura tudu wajen yamma, har zuwa hamadar Bet-awen inda ta ƙare. 13Daga can iyakar ta yi kudu, ta nufi cibiyar Luz, wato Betel, ta gangara zuwa Atarot-addar a bisa dutsen da yake kudu da Bet-horon ta kwari. 14Daga nan iyakar ta nausa ta nufi yammacin kudancin dutse da yake kudu, daura da Bet-horon, sa'an nan ta tsaya a Kiriyat-ba'al, wato Kiriyat-yeyarim, birnin Yahuza. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma. 15A wajen kudu kuwa iyakar ta fara daga karkarar Kiriyat-yeyarim, daga can ta miƙa zuwa Efron a maɓuɓɓugar ruwan Neftowa. 16Iyakar kuma ta gangara zuwa gefen dutsen da yake fuskar kwarin ɗan Hinnon, wanda yake arewa wajen ƙarshen kwarin Refayawa. Ta kuma gangara zuwa kwarin Hinnom ta yi kudu daura da Yebusiyawa, ta gangara zuwa En-rogel. 17Sai ta nausa ta yi wajen arewa zuwa En-shemesh, sa'an nan ta tafi Gelilot wanda yake daura da hawan Adummim. Daga nan ta gangara zuwa Dutsen Bohan, ɗan Ra'ubainu. 18Sai ta wuce ta yi arewa daura da gefen Bet-araba, daga nan ta gangara zuwa Araba. 19Ta kuma zarce zuwa arewa daura da gefen Bet-hogla, ta tsaya a arewacin gaɓar Tekun Gishiri a ƙarshen Urdun wajen kudu. 20Kogin Urdun shi ne iyakar a wajen gabas. Waɗannan su ne iyakokin yankin ƙasar da iyalan kabilar Biliyaminu suka gāda.
21Biranen iyalan kabilar Biliyaminu ke nan Yariko, da Bet-hogla, da Emekkeziz, 22da Bet-araba, da Zemarayim, da Betel, 23da Awwim, da Fara, da Ofra, 24da Kefar-ammoni, da Ofni, da Geba. Birane goma sha biyu ke nan tare da ƙauyukansu. 25Akwai kuma Gibeyon, da Rama, da Biyerot, 26da Mizfa, da Kefira, da Moza, 27da Rekem, da Irfeyel, da Tarala, 28da Zela, da Elef, da Yebus, wato Urushalima, da Gebeya, da Kiriyat. Birane goma sha huɗu ke nan tare da ƙauyukansu. Wannan shi ne rabon gādon mutanen Biliyaminu bisa ga iyalansu.

Currently Selected:

Josh 18: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in