YouVersion Logo
Search Icon

Josh 17

17
1Aka ba kabilar Manassa, ɗan farin Yusufu, nata rabon gādo. Makir ɗan farin Manassa, uban Gileyad, aka ba shi Gileyad da Bashan domin shi jarumi ne. 2Aka kuma raba wa sauran mutanen kabilar Manassa nasu rabon gādo bisa ga iyalansu, wato Abiyezer, da Helek, da Asriyel, da Shekem, da Hefer, da Shemida. Waɗannan su ne 'ya'yan Manassa, maza, bisa ga iyalansu.
3Zelofehad kuwa ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manassa ba shi da 'ya'ya maza, sai dai mata. Sunayensu ke nan, Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza. 4#L.Ƙid 27.1-7 Suka zo wurin Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin, suka ce, “Ubangiji ya umarci Musa ya ba mu gādo tare da 'yan'uwanmu maza.” Sai ya ba su gādo tare da 'yan'uwan mahaifinsu bisa ga umarnin Ubangiji. 5Saboda haka kuwa Manassa ya sami kashi goma banda ƙasar Gileyad da Bashan da yake hayin gabashin Urdun, 6domin jikokin Manassa mata sun sami gādo tare da jikokinsa maza. Aka ba sauran mutanen kabilar Manassa ƙasar Gileyad.
7Yankin ƙasar Manassa ya kai daga Ashiru zuwa Mikmetat wadda take gabas da Shekem. Iyakar kuma ta miƙa kudu zuwa mazaunan En-taffuwa. 8Ƙasar Taffuwa tana hannun mutanen Manassa, amma mutanen Ifraimu ne suke da garin Taffuwa wanda yake iyakar yankin Manassa. 9Iyakar kuma ta gangara zuwa rafin Kana. Waɗannan birane da suke kudancin rafin, na Ifraimu ne, ko da yake suna cikin biranen Manassa. Iyakar Manassa kuwa ta bi gefen arewacin rafin ta gangara a Bahar Rum. 10Ƙasar wajen kudu ta Ifraimu ce, ta wajen arewa kuwa ta Manassa. Bahar Rum ita ce iyakarsu. Mutanen Ashiru suna wajen arewa, mutanen Issaka kuwa wajen gabas. 11A yankin ƙasar Issaka da na Ashiru, Manassa yana da waɗannan wurare, Bet-sheyan da ƙauyukanta, da Ibleyam da ƙauyukanta, da mazaunan Dor da ƙauyukanta, da mazaunan Endor da ƙauyukanta, da mazaunan Ta'anak da ƙauyukanta, da mazaunan Magiddo da ƙauyukanta, da sulusin Nafat. 12#L.Mah 1.27,28 Amma mutanen Manassa ba su iya su mallaki waɗannan birane ba, don haka Kan'aniyawa suka yi zamansu a wuraren. 13Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi ƙarfi sai suka tilasta su su yi musu aikin dole, amma ba su iya korarsu ba.
14Kabilan Yusufu suka ce wa Joshuwa, “Me ya sa ka ba mu rabon gādo guda ɗaya? Ga shi kuwa, muna da jama'a mai yawa, gama Ubangiji ya sa mana albarka.”
15Joshuwa kuwa ya amsa musu, ya ce, “Idan ku babbar jama'a ce, har ƙasar tuddai ta Ifraimu ta kāsa muku, to, sai ku shiga jeji ku sheme wa kanku wuri a ƙasar Ferizziyawa da ta Refayawa.”
16Sai mutanen kabilan Yusufu suka ce, “Ƙasar tuddai ba ta ishe mu ba, ga kuma Kan'aniyawa da suke zaune a filin, da waɗanda suke a Bet-sheyan da ƙauyukanta, da waɗanda suke cikin Kwarin Yezreyel suna da karusan ƙarfe.”
17Joshuwa kuma ya ce wa jama'ar gidan Yusufu, wato kabilar Ifraimu da ta Manassa, “Ku babbar jama'a ce, ga shi kuma, kuna da ƙarfi, ba kashi ɗaya kaɗai za ku samu ba, 18amma ƙasar tuddai kuma za ta zama taku, ko da yake jeji ne. Sai ku sheme, ku mallaka duka. Gama za ku kori Kan'aniyawa, ko da yake su ƙarfafa ne, suna kuma da karusan ƙarfe.”

Currently Selected:

Josh 17: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in