Josh 19
19
Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Saminu
1Kuri'a ta biyu ta faɗa kan kabilar Saminu bisa ga iyalanta. Nasu rabon gādon yana tsakiyar rabon gādon kabilar Yahuza. 2#1Tar 4.28-33 Waɗannan su ne wuraren da suka gāda, Biyer-sheba, da Sheba, da Molada, 3da Hazar-shuwal, da Bilha, da Ezem, 4da Eltola, da Betul, da Horma, 5da Ziklag, da Bet-markabot, da Hazar-susa, 6da Bet-lebawot, da Sharuhen. Garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu. 7Akwai kuma Ayin, da Rimmon, da Eter, da Ashan. Garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu, 8da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da waɗannan garuruwa tun daga Ba'alat-biyer, wato Ramot ta Negeb. Wannan shi ne rabon gādon iyalan kabilar Saminu. 9Gādon kabilar Saminu yana cikin yankin ƙasar rabon kabilar Yahuza domin rabon kabilar Yahuza ya yi mata yawa, don haka kabilar Saminu ta sami gādo daga cikin tsakiyar gādon kabilar Yahuza.
Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Zabaluna
10Kuri'a ta uku ta faɗa a kan kabilar Zabaluna bisa ga iyalanta. Yankin ƙasar gādonsu ya kai har Sarid. 11Iyakar ta hau wajen yamma zuwa Marala, ta kai Dabbeshet da rafin da yake gabas da Yakneyam. 12Daga Sarid, ta nufi wajen gabas zuwa iyakar Kislotabar, sa'an nan ta bi ta Daberat da Yafiya. 13Daga can ta miƙa wajen gabas zuwa Gat-hefer da Et-kazin, har zuwa Rimmon inda ta nausa zuwa Neya. 14Daga wajen arewa iyakar ta juya zuwa Hannaton, sa'an nan ta faɗa a kwarin Iftahel. 15Waɗannan garuruwa, da Kattat, da Nahalal, da Shimron, da Idala, da Baitalami, suna cikin garuruwa goma sha biyu da ƙauyukansu da suke cikin yankin ƙasar kabilar Zabaluna. 16Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke cikin gādon mutanen Zabaluna bisa ga iyalansu.
Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Issaka
17Kuri'a ta huɗu ta faɗo a kan kabilar Issaka bisa ga iyalanta. 18Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar su ne, Yezreyel, da Kesullot, da Shunem, 19da Hafarayim, da Shiyon, da Anaharat, 20da Rabbit, da Kishiyon, da Ebez, 21da Remet da En-ganim, da En-hadda, da Bet-fazzez. 22Iyakar kuma ta bi ta Tabor, da Shahazuma, da Bet-shemesh. Sa'an nan ta gangara a Kogin Urdun. Akwai garuruwa goma sha shida da ƙauyukansu. 23Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke a yankin ƙasar da kabilar Issaka ta gāda bisa ga iyalanta.
Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Ashiru
24Kuri'a ta biyar ta fāɗo a kan kabilar Ashiru bisa ga iyalanta. 25Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar, su ne Helkat, da Hali, da Beten, da Akshaf, 26da Alammelek, da Amad, da Mishal. A wajen yamma, iyakar ta bi ta Karmel da Shihor-libnat. 27Daga nan sai ta nausa wajen gabas, ta bi ta Bet-dagon, da Zabaluna, da kwarin Iftahel a wajen arewa zuwa Bet-emek da Nayil. Ta yi gaba a wajen arewa zuwa Kabul, 28da Hebron, da Rehob, da Hammon, da Kana, har ta bi ta Sidon Babba. 29Daga can ta nausa zuwa Rama, ta bi ta garun birnin Taya, sai kuma ta nausa zuwa Hosa, sa'an nan ta gangara Bahar Rum, wajen Mahalab, da Akzib, 30da Umma, da Afek, da Rehob. Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu. 31Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke cikin yankin ƙasar da kabilar Ashiru ta gāda bisa ga iyalanta.
Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Naftali
32Kuri'a ta shida ta faɗo a kan kabilar Naftali bisa ga iyalanta. 33Tasu iyaka, ta miƙa daga Helef, daga itacen oak da yake cikin Za'anannim, da Adami-nekeb, da Yabneyel har zuwa Lakkum, sa'an nan ta tsaya a Kogin Urdun. 34Iyakar kuma ta juya wajen kudu zuwa Aznot-tabor, daga can ta miƙa zuwa Hukkok, sa'an nan ta kai Zabaluna wajen kudu, da Ashiru wajen yamma, da Yahuza wajen gabas wajen Urdun. 35Garuruwan da yake da garu su ne, Ziddim, da Zer, da Hammat, da Rakkat, da Kinneret, 36da Adama, da Rama, da Hazor, 37da Kedesh, da Edirai, da En-hazor, 38da Iron, da Migdal-el, da Horem, da Bet-anat, da Bet-shemesh. Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu. 39Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon gādon kabilar Naftali da iyalanta.
Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Dan
40Kuri'a ta bakwai ta faɗo a kan kabilar Dan bisa ga iyalanta. 41Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar gādonta ke nan, da Zora, da Eshtawol, da Ir-shemesh, 42da Shalim, da Ayalon, da Itla, 43da Elon, da Timna, da Ekron, 44da Elteki, da Gebbeton, da Ba'alat, 45da Yahud, da Bene-berak, da Gat-rimmon, 46da Meyarkon, da Rakkon, tare da karkarar da take gefen Yaffa. 47#L.Mah 18.27-29 Sa'ad da Danawa suka rasa karkararsu, suka tafi, suka yaƙi Leshem. Da suka ci ta, sai suka hallaka mutanenta da takobi, suka mallaki ƙasar, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato Dan. 48Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon kabilar Dan bisa ga iyalanta.
Yankin Ƙasar da aka Ba Joshuwa
49Sa'ad da mutanen Isra'ila suka gama rarraba gādon ƙasar, suka ba Joshuwa ɗan Nun nasa rabo a cikin nasu. 50Bisa ga umarnin Ubangiji, suka ba shi garin da ya roƙa, wato Timnatsera a ƙasar tudu ta Ifraimu. Ya sāke gina garin, ya kuwa zauna a ciki.
51Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin kakannin gidajen kabilan jama'ar Isra'ila, suka rarraba ta hanyar jefa kuri'a a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada a Shilo. Ta haka suka gama rarraba ƙasar.
Currently Selected:
Josh 19: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979