Ayu 8
8
Bildad Ya Ƙarfafa Hukuncin Allah Daidai Ne
1Sai Bildad ya yi magana.
2“Ka gama maganganunka marasa kan gado duka?
3Allah bai taɓa yin danniya ba,
Bai kuma taɓa fāsa aikata abin da yake daidai ba.
4Lalle 'ya'yanka sun yi wa Allah zunubi,
Don haka ya hukunta su yadda ya cancanta.
5Amma sai ka juyo ka yi roƙo ga Allah Maɗaukaki.
6Idan kana da tsarki da aminci, Allah zai taimake ka,
Ya maido da iyalin gidanka, ya yi maka sakayya.
7Duk hasarar dukiyan nan da ka yi, ba kome ba ne
In aka gwada da abin da Allah zai ba ka nan gaba.
8“Ka tsai da zuciyarka a kan hikima irin ta zamanin dā.
Ka kuma yi ta yin tunani a kan gaskiyar da kakanninmu suka koya.
9Kwanakinmu 'yan kaɗan ne kawai,
Ba mu san kome ba,
Mu inuwa ne kawai a fuskar duniya.
10Amma ka yarda masu hikima na zamanin dā su koya maka,
Ka kasa kunne ga abin da za su faɗa.
11“Iwa ba ta tsirowa inda ba ruwa,
Ba a taɓa samunta a ko'ina ba sai a fadama.
12In ruwan ta ƙafe, ita ce za ta fara bushewa,
Tun tana ƙanƙana ba ta isa a yanke a yi amfani da ita ba.
13Marasa tsoron Allah kamar iwan nan suke,
Ba su da sa zuciya muddin sun rabu da Allah.
14Suna dogara ga silin zare, murjin gizo-gizo.
15Idan suka jingina ga saƙar gizo-gizo, za ta iya tokare su?
Idan sun kama ta, za ta taimake su tsayawa?
16“Mugaye sukan tsiro kamar ciyayi a hasken rana,
Ciyayin da sukan yaɗu su cinye gona duka.
17Saiwoyinsu sukan nannaɗe duwatsu,
Su riƙe kowane dutse da ƙarfi.
18Amma idan aka tumɓuke su,
Ba wanda zai taɓa cewa sun kasance a wurin.
19Hakika matuƙar murnar da mugaye suke da ita ke nan,
Yanzu waɗansu ne za su zo su gāje wurarensu.
20“Amma daɗai Allah ba zai rabu da amintattu ba,
Ba kuwa zai taɓa taimakon mugun mutum ba.
21Zai sāke barinka ka yi dariya ka ƙyalƙyata kamar dā,
Ka kuma yi sowa da murna matuƙa.
22Amma zai sa maƙiyanka su sha kunya,
Za a shafe gidajen mugaye.”
Currently Selected:
Ayu 8: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979