Ayu 3
3
Ayuba Ya Kai Kuka ga Allah
1 #
Irm 20.14-18
Ayuba ya yi magana ya la'anci ranar da aka haife shi.
2Ya ce,
“Ya Ubangiji, ka la'anci ranan nan da aka haife ni.
3Ka la'anci daren nan da aka yi cikina.
4Ka mai da ranan nan ta zama duhu, ya Allah.
Kada a ƙara tunawa da wannan rana,
Kada haske ya ƙara haskakata.
5Ka sa ta zama ranar duhu baƙi ƙirin.
Ka rufe ta da gizagizai, kada hasken rana ya haskaka ta.
6Ka shafe wannan dare daga cikin shekara,
Kada kuma a ƙara lasafta shi.
7Ka sa daren ya zama marar amfani, daren baƙin ciki.
8Ka faɗa wa masu sihiri su la'anci wannan rana,
Su waɗanda suke umartar dodon ruwa.
9Ka hana gamzaki haskakawa,
Kada ka bar daren nan ya sa zuciya ga wayewar gari,
10Ka la'anci daren nan da aka haife ni,
Da ya jefa ni a baƙin ciki da wahala.
11“Da ma na mutu tun a cikin cikin uwata,
Ko kuwa da haihuwata in mutu.
12Me ma ya sa uwata ta rungume ni a ƙirjinta,
Ta shayar da ni kuma da mamanta?
13Da a ce na mutu a lokacin, da yanzu ina huce,
14Da ina ta barcina kamar sarakuna da masu mulki
Waɗanda suka sāke gina fādodi na dā,
15Da ina ta sharar barcina kamar shugabanni
Waɗanda suka cika gidajensu da zinariya da azurfa,
16In yi ta sharar barci kamar jariran da aka haifa matattu.
17Mugaye za su daina muguntarsu a kabari,
Ma'aikatan da suka gaji da aiki su ma za su huta,
18Har 'yan sarƙa ma za su ji daɗin salama,
Su huta daga tsautawa da umarnai masu tsanani.
19Kowa da kowa yana wurin, babba da ƙarami duk ɗaya ne,
Bayi ma sun sami 'yanci.
20“Me ya sa ake barin mutane su yi ta zama cikin damuwa?
Me ya sa ake ba da haske ga waɗanda suke baƙin ciki?
21 #
W.Yah 9.6
Sun jira mutuwa, amma ta ƙi samuwa,
Sun fi son kabari da kowace irin dukiya.
22Ba su da farin ciki, sai sun mutu an binne su tukuna.
23Allah ya ɓoye musu sanin abin da zai faru nan gaba,
Ya kalmashe su kowane gefe.
24A maimakon cin abinci, sai baƙin ciki nake yi,
Ba kuma zan daina yin nishi ba,
25Dukan abin da nake jin tsoro ko fargaba ya faru.
26Ba ni da salama, ba ni da hutawa,
Wahala ba za ta taɓa ƙarewa ba.”
Currently Selected:
Ayu 3: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979