Ayu 31
31
Ayuba Ya Tabbatar da Mutuncinsa
1“Na yi alkawari da idanuna,
Me zai sa in ƙyafaci budurwa?
2Wane rabo zan samu daga wurin Allah a Sama?
Wane gādo kuma zan samu daga wurin Mai Iko Dukka a can samaniya?
3Yakan aika da masifa da lalacewa
Ga waɗanda suke aikata abin da ba daidai ba.
4Allah ya san dukan abin da nake yi,
Yana ƙididdige dukan takawata.
5“Idan ina tafiya da rashin gaskiya,
Ina hanzari don in aikata yaudara,
6Bari Allah ya auna ni da ma'aunin da yake daidai,
Zai kuwa san mutuncina.
7Idan dai na kauce daga hanya,
Ko kuwa zuciyata ta bi sha'awar idanuna,
Idan akwai ko ɗan sofane a hannuna,
8To, bari in shuka, wani ya ci amfanin,
Bari a tumɓuke amfanin gonata.
9“Idan na yi sha'awar wata mace,
Har na je na laɓe a ƙofar maƙwabcina,
10To, bari matata ta yi wa wani abinci,
Bari waɗansu su kwana da ita.
11Gama wannan mugun laifi ne ƙwarai,
Wanda alƙalai ne za su hukunta.
12Za ta zama wuta mai ci har ta hallaka,
Za ta cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.
13“Idan a ce ban kasa kunne ga kukan barorina mata da maza ba,
Sa'ad da suka kawo koke-kokensu a kaina,
14To, wace amsa zan ba Allah sa'ad da ya tashi don ya hukuntar?
Me zan iya faɗa sa'ad da Allah ya zo yi mini shari'a?
15Ashe, shi wanda ya halicce ni a cikin mahaifa,
Ba shi ne ya halicce su ba?
Shi wanda ya siffata mu a cikin mahaifa?
16“Ban taɓa ƙin taimakon matalauta ba,
Ban kuma taɓa sa gwauruwar da mijinta ya mutu ta yi kuka ba,
17Ko kuwa in bar marayu da yunwa sa'ad da nake cin abincina,
18Tun suna yara nake goyonsu,
Ina lura da su kamar 'ya'yan cikina.
19“Amma idan na ga wani yana lalacewa saboda rashin sutura,
Ko wani matalauci marar abin rufa,
20Idan a zuciyarsa bai sa mini albarka ba,
Ko bai ji ɗumi da ulun tumakina ba,
21Ko na ɗaga hannuna don in cuci maraya,
Don na ga ina da kafar kuɓuta,
22To, ka sa kafaɗuna su ɓaɓɓalle daga inda suke.
Ka kakkarya gwiwoyin hannuna.
23Gama bala'i daga wurin Allah ya razanar da ni,
Saboda ɗaukakarsa ba zan iya yin kome ba.
24“Idan na ce ga zinariya na dogara, ko zinariya tsantsa ita ce jigona,
25Idan kuma saboda yawan dukiyata nake fariya,
Ko saboda abin da na mallaka ne,
26Idan ga hasken rana nake zuba ido,
Ko ga hasken farin wata ne,
27Zuciyata ta jarabtu ke nan a asirce,
Ni da kaina ina sumbatar hannuna,
28Wannan ma zai zama laifi ne wanda alƙalai za su hukunta,
Gama na zama munafukin Allah Mai Iko Dukka ke nan.
29“Idan na yi murna saboda wahala ta sami maƙiyana,
Ko na yi fariya saboda mugun abu ya same shi,
30Ban yi zunubi da bakina ba,
Ban nemi ran wani ta wurin la'anta shi ba.
31Ko mutanen da suke cikin alfarwata ba wanda zai ce,
Ga wani can da bai ƙoshi da nama ba.
32Ban bar baƙi su kwana a titi ba,
Ƙofar gidana a buɗe take ga matafiya.
33Idan na ɓoye laifofina a zuciyata,
34Ko na tsaya shiru saboda tsoron taron jama'a,
Saboda kuma baƙar maganar mutane ta razanar da ni.
35“Da a ce ina da wanda zai kasa kunne gare ni,
Da sai in sa hannu a kan abin da na faɗa,
Allah kuwa Mai Iko Dukka ya amsa mini.
“Da ƙarar da maƙiyana suke kai ni, a rubuce ne,
36Hakika da sai in ɗauke ta a kafaɗata,
In kuwa naɗa ta a kaina kamar rawani.
37Da na ba Allah dukan lissafin abin da na taɓa yi,
In tinƙare shi kamar ni basarauce ne.
38“Idan ƙasata tana kuka da ni,
Ita da kunyoyinta,
39Ko na ci amfaninta ban biya ba,
Ko na yi sanadin mutuwar mai ita,
40Ka sa ƙayayuwa su tsiro maimakon alkama,
Tsire-tsire marasa amfani kuma maimakon sha'ir.”
Maganar Ayuba ta ƙare.
Currently Selected:
Ayu 31: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979