Ayu 30
30
Ayuba Ya Yi Kuka saboda Masifunsa
1“Amma yanzu waɗanda na girme su, sai ba'a suke mini,
Waɗanda iyayensu maza ba su fi karnukan da suke kiwon garken tumakina ba.
2Wace riba zan samu ta wurin ƙarfin hannuwansu waɗanda ba su da sauran kuzari?
3Saboda rashi da matsananciyar yunwa sun rame,
Sai gaigayar ƙasa suke yi da dare, a cikin kufai.
4Sukan tsinki ganyaye masu ɗaci na jeji su ci,
Sukan ci doyar jeji.
5Aka kore su daga cikin mutane,
Suka yi ta binsu da ihu kamar yadda ake yi wa ɓarawo,
6Sai a kwazazzabai suke zama
Da a ramummuka da kogwannin duwatsu.
7Suka yi ta kuka a jeji,
Suka taru wuri ɗaya a cikin sarƙaƙƙiya.
8Mutane ne marasa hankali marasa suna!
Aka kore su daga ƙasar.
9“Yanzu na zama abin waƙa gare su,
Abin ba'a kuma a gare su.
10Suna ƙyamata, guduna suke yi,
Da ganina, sai su tofa mini yau.
11Domin Allah ya katse lakata, ya ƙasƙanta ni,
Saboda haka sun raba ni da zuriyata,
12A hannun dama 'yan tā da zaune tsaye sun taso mini,
Sun runtume ni, sun tura ni a hanyarsu ta hallakarwa.
13Sun datse hanyata,
Sun jawo mini bala'i,
Ba kuwa wanda ya hana su.
14Sun kutsa kamar waɗanda suka karya doka,
Sun auka mini da dukan ƙarfinsu kamar yadda suka yi nufi.
15Sun firgita ni,
Sun kori darajata kamar da iska,
Wadatata kuma ta shuɗe kamar girgije.
16“Yanzu zuciyata ta narke
Kwanakin wahala sun same ni.
17Da dare ƙasusuwana karkaɗuwa suke,
Azaba tana ta gaigayata ba hutawa.
18An yi mini kamun kama-karya,
An ci wuyan rigata.
19Allah ya jefar da ni cikin laka,
Na zama kamar ƙura ko toka.
20“Na yi kira gare ka, ya Allah, amma ba ka amsa mini ba,
Na yi addu'a kuma, amma ba ka kula da ni ba.
21Ka zama mugu a gare ni,
Da ƙarfin dantsenka ka tsananta mini.
22Ka jefa ni cikin guguwa, ka sa ni in hau ta,
Ka yi ta shillo da ni cikin rugugin hadiri.
23Hakika na sani za ka kai ni ga mutuwa,
Gidan da aka ƙaddara wa kowane mai rai.
24“Ashe, wanda yake gab da gagarumar hallaka,
Ba zai miƙa hannu ya roƙi taimako a masifar da yake sha ba?
25Ashe, ban yi kuka saboda wanda yake shan wahala ba?
Ashe, ban yi ɓacin rai saboda matalauta ba?
26Amma sa'ad da na sa zuciya ga alheri, sai ga mugunta,
Sa'ad da nake jiran haske, sai ga duhu ya zo.
27Zuciyata tana tafasa, ba ta kwanciya,
Kwanakin wahala sun auko mini.
28Na yanƙwane, amma ba yanƙwanewar rana ba,
Na tsaya a gaban taron jama'a, ina roƙon taimako.
29“Na zama ɗan'uwan dila,
Na kuma zama aminin jiminai.
30Fatata ta takura, ta zama baƙa,
Ƙasusuwana suna zogi saboda zafi,
31Saboda haka garayata ta zama ta makoki,
Sarewata kuma ta zama muryar masu kuka.”
Currently Selected:
Ayu 30: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979