Bible App logo
Search Icon

Ayu 29

29
Ayuba Ya Tuno da Farin Cikinsa na Dā
1Ayuba ya ci gaba da magana.
2Da ma ina cikin lokacin da ya wuce ne,
Lokacin da Allah yake lura da ni,
3Sa'ad da fitilarsa take haskaka mini,
Ta wurin haskensa kuma nake tafiya da duhu,
4Kwanakin da nake gaɓar raina,
Lokacin da ni'imar Allah take kan gidana,
5Sa'ad da Mai Iko Dukka yake tare da ni,
'Ya'yana duka kuma suka kewaye ni,
6Sa'ad da aka wanke ƙafafuna da madara,
Duwatsu kama suna ɓulɓulo mini da rafuffukan mai!
7A sa'ad da nakan tafi kofar birni,
In shirya wurin zamana a dandali,
8Da samari sun gan ni, sai su kawar da jiki,
Tsofaffi kuma su miƙe tsaye,
9Sarakuna sun yi shiru sun kame bakinsu.
10Manyan mutane sukan yi shiru, harshensu ya liƙe a dasashi.
11Waɗanda suka ji labarina sukan sa mini albarka,
Waɗanda suka gan ni sukan yi na'am da ni.
12Domin sa'ad da matalauta suka yi kuka, ni nake cetonsu,
Nakan taimaki marayu waɗanda ba su da mai taimako.
13Waɗanda suke bakin mutuwa sukan sa mini albarka,
Na taimaki gwaurayen da mazansu suka mutu,
Su raira waƙa don murna.
14Adalci shi ne suturata,
Gaskiya ita ce rigata da rawanina.
15Ni ne idon makafi, guragu kuma, ni ne ƙafarsu.
16Ni mahaifi ne ga matalauta,
Nakan bincika don in warware al'amarin da ya dami baƙi.
17Nakan karya muƙamuƙin marar adalci,
In sa yă saki ganimar da yă kama.
18“Da na zaci zan mutu cikin sutura,
Kwanakina kuma su riɓaɓɓanya, su yi yawa kamar yashi,
19Saiwoyina a shimfiɗe suke cikin ruwa,
Dukan dare raɓa na sauka a kan rassana.
20Darajata garau take a gare ni,
Bakana kullum sabo yake a hannuna.
21Mutane sukan kasa kunne su jira, su yi shiru
Sa'ad da nake ba da shawara.
22Bayan na gama magana ba wanda zai ƙara wata magana.
Maganata takan shige su.
23Suna jirana kamar yadda ake jiran ruwan sama,
Da baki buɗe, kamar yadda ake jiran ruwan bazara.
24Nakan yi musu murmushi sa'ad da suka fid da zuciya,
Ba su yi watsi da fara'ata ba.
25Nakan zaɓar musu hanyar da za su bi,
Ina zaune kamar sarki a tsakanin mayaƙansu,
Kamar mai ta'azantar da masu makoki.”

Currently Selected:

Ayu 29: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in