YouVersion Logo
Search Icon

Ayu 16

16
Ayuba Ya Yi Kukan abin da Allah Yake Yi
1Ayuba ya yi magana.
2“Ai, na taɓa jin magana irin wannan,
Ta'aziyyar da kake yi azaba ce kawai.
3Ka dinga yin magana ke nan har abada?
A kullum maganarka ita ce dahir?
4In da a ce a matsayina kake, ni kuma ina a naka,
Ina iya faɗar duk abin da kake faɗa yanzu.
Da sai in kaɗa kaina da hikima,
In dulmuyar da kai a cikin rigyawar maganganu.
5Da sai in ba ka shawara ta ƙarfafawa,
In yi ta yi maka maganar ta'azantarwa.
6“Amma ba abin da zan faɗa wanda zai taimaka,
Yin shiru kuma ba zai raba ni da azaba ba.
7Ka gajiyar da ni, ya Allah,
Ka shafe iyalina.
8Ka kama ni, kai maƙiyina ne.
Na zama daga fata sai ƙasusuwa,
Mutane suka ɗauka, cewa wannan ya tabbatar ni mai laifi ne.
9Allah ya kakkarya gaɓoɓina da fushinsa,
Yana dubana da ƙiyayya.
10Mutane sun buɗe baki don su haɗiye ni
Suna kewaye ni suna ta marina.
11Allah ya bashe ni ga mugaye.
12Dā ina zamana da salama,
Amma Allah ya maƙare ni,
Ya fyaɗa ni ƙasa ya ragargaza ni.
Allah ya maishe ni abin bārata.
13Ya harbe ni da kibau daga kowane gefe.
Kiban sun ratsa jikina sun yi mini rauni,
Duk da haka bai nuna tausayi ba!
14Ya yi ta yi mini rauni a kai a kai,
Ya fāɗa mini kamar soja da ƙiyayya ta haukata.
15“Ina makoki saye da tsummoki,
Ina zaune cikin ƙura a kunyace.
16Na yi ta kuka har fuskata ta zama ja wur,
Idanuna kuma suka yi luhuluhu.
17Amma ban yi wani aikin kama-karya ba,
Addu'ata ga Allah kuwa ta gaskiya ce.
18“Duniya, kada ki ɓoye laifofin da aka yi mini!
Kada ki yi shiru da roƙon da nake yi na neman adalci!
19 # Ayu 19.25 Akwai wani a Sama
Wanda zai tsaya mini ya goyi bayana.
20Ina so Allah ya ga hawayena,
Ya kuma ji addu'ata.
21“Ina so wanda zai yi roƙo ga Allah domina,
Kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.
22Yanzu shekaruna wucewa suke yi,
Ina bin hanyar da ba a komawa.”

Currently Selected:

Ayu 16: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in