Ayu 15
15
Elifaz Ya Tsauta wa Ayuba
1Elifaz ya yi magana.
2“Surutai, Ayuba! Surutai!
3Ba wani mai hikima wanda zai yi magana irin taka,
Ko kuma ya kāre kansa da irin maganganun da ba su da ma'ana.
4Kana karya jama'a, kana hana su jin tsoron Allah,
Kana hana su yin addu'a gare shi.
5Mugun lamirinka shi ne yake magana yanzu,
Kana ƙoƙari ka ɓuya a bayan maganganunka na wayo.
6Ba na bukata in kā da kai,
Kowace kalma da ka hurta ta kā da ka.
7“Kana tsammani kai ne mutumin da aka haifa na farko?
Sa'ad da Allah ya yi duwatsu kana nan?
8Ko ka taɓa jin shirye-shiryen da Allah ya yi?
Ko kai kaɗai kake da hikima a cikin mutane?
9Ba wani abu da ka sani da mu ba mu sani ba.
10Daga wurin mutanen da suka yi furfura muka koyi hikimarmu.
Mun koyi hikimarmu daga mutane waɗanda aka haife su
Tun kafin a haifi mahaifinka.
11“Allah yana ta'azantar da kai,
Me ya sa har yanzu ka ƙi kulawa da shi?
Mun yi magana a madadinsa a natse da lafazi mai daɗi.
12Amma ka ta da hankalinka,
Kana ta zazzare mana ido da fushi.
13Fushi kake yi da Allah, kana ƙinsa.
14 #
Ayu 25.4-6
Akwai mutumin da yake tsarkakakke sarai?
Akwai mutumin da yake cikakke a wurin Allah?
15Me ya sa Allah bai sakar wa mala'ikunsa kome ba?
Har su ma ba tsarkaka suke a gare shi ba.
16Mutum yakan sha mugunta kamar yadda yake shan ruwa,
Hakika mutum ya lalace, ya zama mai rainako.
17“Yanzu ka saurara, ya Ayuba, ga abin da na sani.
18Mutane masu hikima sun koya mini gaskiya
Wadda suka koya daga wurin kakanninsu,
Ba su kuwa ɓoye mini asirin kome ba.
19Ƙasaru 'yantacciya ce daga baƙi
Ba wanda zai raba su da Allah.
20“Mugun mutum mai zaluntar sauran mutane
Zai kasance da wahala muddin ransa.
21Zai ji ƙarar muryoyi masu firgitarwa a kunnuwansa.
'Yan fashi za su fāɗa masa
Sa'ad da yake tsammani ba abin da zai same shi.
22Bai sa zuciya zai kuɓuta daga duhu ba,
Gama takobi yana jiransa a wani wuri don ya kashe shi.
23Yana ta yawon neman abinci, yana ta cewa, ‘Ina yake?’
Ya sani baƙin ciki ne yake jiransa a nan gaba. Kamar sarki mai iko,
24Haka masifa take shirin fāɗa masa.
25“Wannan shi ne ƙaddarar mutum,
Wanda ya nuna wa Allah yatsa,
Ya kuwa raina Mai Iko Dukka.
26Wannan mutum mai girmankai ne, ɗan tawaye.
27Ya ɗauki garkuwarsa kamar ɗan yaƙi,
Ya ruga don ya yi yaƙi da Allah.
28Shi ne mutumin da ya ci birane da yaƙi,
Ya ƙwace gidajen waɗanda suka tsere,
Amma yaƙi ne zai hallaka birane da gidaje.
29Arzikinsa ba zai daɗe ba,
Duk abin da ya mallaka ba zai daɗe ba.
Har inuwarsa ma za ta shuɗe,
30Ba kuwa zai kuɓuta daga duhu ba.
Zai zama kamar itacen da wuta ta ƙone rassansa,
Kamar itace kuma da iska ta kaɗe furensa.
31Idan wauta tasa ta kai shi ga dogara ga mugunta,
To, mugunta ce kaɗai zai samu.
32Kafin kwanakinsa su cika zai bushe,
Zai bushe kamar reshe, ba zai ƙara yin ganye ba.
33Zai ama kamar itacen inabi
Wanda 'ya'yansa suka kakkaɓe tun kafin su nuna,
Kamar itacen zaitun wanda bai taɓa yin 'ya'ya ba.
34Marasa tsoron Allah ba za su sami zuriya ba,
Wuta za ta cinye gidajen da aka gina da dukiyar rashawa.
35Waɗannan su ne irin mutanen da suke shirya tarzoma, su aikata mugunta.
Kullum zuciyarsu cike take da ruɗarwa.”
Currently Selected:
Ayu 15: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979