YouVersion Logo
Search Icon

Ayu 13

13
Ayuba Ya Kāre Mutuncinsa
1-2Duk abin da ka hurta, na taɓa jinsa,
Na gane da shi sarai.
Iyakar abin da kuka sani, ni ma na sani.
Ba ku fi ni da kome ba.
3Amma da Allah nake jayayya, ba da ku ba,
Ina so in yi muhawara da shi a kan ƙarar da nake da ita.
4Kun ɓoye jahilcinku da ƙarairayi.
Kun zama kamar likitoci waɗanda ba su iya warkar da kowa ba.
5Kada ku faɗi kome,
Wani sai ya ce kuna da hikima!
6“Ku saurara mini, zan faɗi ƙarata.
7Me ya sa kuke yin ƙarya?
Kuna tsammani ƙarairayinku za su taimaki Allah?
8Son zuciya kuke yi, ko ba haka ba?
Kuna goyon bayan Allah?
Za ku goyi bayan Allah sa'ad da aka gurfanar da ni gaban shari'a?
9Da Allah ya bincike ku sosai,
Zai iske wani abin kirki ne a cikinku?
Kuna tsammani za ku ruɗi Allah, kamar yadda kuke ruɗin mutane?
10Ko da yake kun ɓoye son zuciyarku,
Duk da haka zai tsauta muku,
11Ikonsa kuwa zai razana ku.
12Karin maganarku da muhawararku ba su da ƙarfi ƙwarai.
13“Ku yi shiru ku ba ni zarafi in yi magana.
Duk abin da zai faru, ya faru.
14A shirye nake in yi kasai da raina.
15Na fid da zuciya ɗungum.
To, in Allah ya kashe ni, sai me?
Zan faɗa masa ƙarata.
16Mai yiwuwa ne ƙarfin halina ya cece ni,
Tun da yake ba wani mugun mutumin da zai iya zuwa gaban Allah.
17Sai a saurari bayanin da zan yi.
18A shirye nake in faɗi ƙarata,
Domin na sani ina da gaskiya.
19“Ya Allah, za ka yi ƙarata?
Idan kuwa ka yi, to, a shirye nake in yi shiru in mutu.
20Ina da abu biyu da zan yi maka roƙo,
Ka yarda da su, sa'an nan ba zan yi ƙoƙari in ɓoye ba.
21Wato ka daina hukuncin da kake yi mini,
Kada ka sa razanarka ta ragargaza ni.
22“Ka fara yin magana, ya Allah, ni kuwa zan amsa.
Ko kuma ka bari in yi magana, sa'an nan ka amsa mini.
23Kuskure da laifi guda nawa na yi?
Waɗanne irin laifofi ake tuhumata da su?
24“Me ya sa kake guduna?
Me ya sa ka maishe ni kamar maƙiyi?
25Ƙoƙari kake ka firgita ni?
Ni ba wani abu ba ne, ganye ne kawai,
Ka fāɗa wa tattaka da yaƙi ne kawai.
26Ka kawo mugayen ƙararraki a kaina,
Har da laifofin da na yi na ƙuruciya.
27 # Ayu 33.11 Ka ɗaure ƙafata da sarƙoƙi,
Kakan lura da kowace takawata,
Har kana bin diddigin sawayena.
28Saboda wannan na zama abin kallo,
ni kuwa kamar ragargazajjen itace ne, ko diddigaggiyar riga.”

Currently Selected:

Ayu 13: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in