YouVersion Logo
Search Icon

Ayu 12

12
Ayuba Ya Ƙarfafa Ikon Allah da Hikimar Allah
1Ayuba ya amsa.
2“Aha! Ashe, kai ne muryar jama'a,
Idan ka mutu hikima ta mutu ke nan tare da kai.
3Amma ni ma ina da hankali gwargwado, kamar yadda kake da shi,
Ban ga yadda ka fi ni ba.
Kowa ya san sukan abin da ka faɗa.
4Har abokaina ma, suna ta yi mini dariya yanzu,
Suna ta dariya ko da yake ni adali ne marar laifi,
Amma akwai lokacin da Allah ya amsa addu'o'ina.
5Ba ka shan wahalar kome, duk da haka ka maishe ni abin dariya.
Ka bugi mutumin da yake gab da fāɗuwa.
6Amma ɓarayi da marasa tsoron
Allah suna zaune cikin salama,
Ko da yake ƙarfinsu ne kaɗai allahnsu.
7“Don haka tsuntsaye da dabbobi sun fi ka sani,
Suna da abu mai yawa da za su koya maka.
8Ka roƙi talikan da suke a duniya, da cikin teku, hikimar da suke da ita.
9Dukansu sun sani ikon Ubangiji ne ya yi su.
10Allah shi ne yake bi da rayukan talikansa.
Numfashin dukan mutane kuwa a ikonsa yake.
11Amma kamar yadda harsunanku suke jin daɗin ɗanɗanar abinci,
Haka nan kuma kunnuwanku suke jin daɗin sauraren kalmomi.
12-13“Tsofaffi suna da hikima,
Amma Allah yana da hikima da iko.
Tsofaffi suna da tsinkaya,
Amma Allah yana da tsinkaya da ikon aikatawa.
14Sa'ad da Allah ya rurrushe, wa zai iya sāke ginawa?
Wa kuma zai iya fitar da mutumin da Allah ya sa a kurkuku?
15Akan yi fari sa'ad da Allah ya hana ruwan sama,
Rigyawa takan zo sa'ad da ya kwararo ruwa.
16Allah mai iko ne a kullum kuwa cikin nasara yake
Da macuci, da wanda aka cutar, duk ƙarƙashin ikon Allah suke.
17Yakan mai da hikimar masu mulki wauta,
Yakan mai da shugabanni marasa tunani.
18Yakan tuɓe sarakuna ya sa su kurkuku.
19Yakan ƙasƙantar da firistoci da mutane masu iko.
20Yakan rufe bakin waɗanda aka amince da su.
Yakan kawar da hikimar tsofaffi.
21Yakan kunyatar da masu iko,
Ya hana wa masu mulki ƙarfi.
22Yakan aika da haske a wuraren da suke da duhu kamar mutuwa.
23Yakan sa sauran al'ummai su yi ƙarfi su ƙasaita,
Sa'an nan ya fatattaka su, ya hallaka su.
24Yakan sa shugabanninsu su zama wawaye,
Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata,
25Su yi ta lalube cikin duhu, su yi ta tangaɗi kamar bugaggu.”

Currently Selected:

Ayu 12: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in