YouVersion Logo
Search Icon

Irm 33

33
Komo da Harka a Urushalima
1Ubangiji ya sāke yin magana da Irmiya sa'ad da yake a kulle a gidan waƙafi. 2Ubangiji wanda ya halitta duniya, ya siffata ta, ya kafa ta, sunansa Ubangiji, ya ce, 3“Ka kira ni, ni kuwa zan amsa maka, zan kuwa nuna maka manyan al'amura masu girma da banmamaki, waɗanda ba ka sani ba.” 4Gama haka Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya ce, a kan gidajen da suke a wannan birni, da gidajen sarakunan Yahuza, waɗanda aka rurrushe domin a yi wa garukan jigo saboda mahaurai da suka kewaye birni, da kuma saboda yaƙi. 5“Sa'ad da ake zuwa yaƙi da Kaldiyawa gidaje za su cika da gawawwakin mutane waɗanda na kashe da fushina da hasalata, gama na ɓoye wa wannan birni zatina saboda dukan muguntarsu. 6Ga shi, zan kawo wa birnin lafiya, gama zan warkar da su, in wadata su da salama da gaskiya. 7Zan kuma mayar wa mutanen Yahuza da mutanen Isra'ila da arzikinsu, in sāke kafa su kamar yadda suke a dā. 8Zan shafe dukan laifin da suka yi mini, in kuma gafarta musu dukan zunubansu da tayarwar da suka yi mini. 9Sunan wannan birni zai zama mini abin murna, da abin yabo, da darajantawa ga dukan al'umman duniya waɗanda za su ji dukan alherin da na yi dominsu, za su ji tsoro su yi rawar jiki saboda dukan alheri da dukan wadata da na tanada musu.”
10Haka Ubangiji ya faɗa, “A wannan wuri da ka ce ya zama kufai, ba mutum ko dabba, wato a biranen Yahuza da titunan Urushalima, inda ba kowa, ba mutum ko dabba a ciki, 11#1Tar 16.34; 2Tar 5.13; 7.3; Ezra 3.11; Zab 100.5; 106.1; 107.1; 118.1; 136.1 za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa,
“ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai
Runduna,
Gama Ubangiji nagari ne,
Gama madawwamiyar ƙaunarsa
tabbatacciya ce.’
“Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”
12Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Wannan wuri wanda yake kufai, inda ba mutum ko dabba, da cikin dukan biranensa, zai sāke zama makiyaya, inda masu kiwo za su zauna da garkunansu. 13A garuruwan ƙasar tuddai, da na kwaruruka, da na Negeb, da na ƙasar Biliyaminu, da na wuraren da suke kewaye da Urushalima, da na Yahuza, garkuna za su sāke bi ta ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,” in ji Ubangiji.
14 # Irm 23.5,6 “Ga shi, kwanaki suna zuwa sa'ad da zan cika alkawarin da na yi wa mutanen Isra'ila da na Yahuza. 15A waɗannan kwanaki da a lokacin nan, zan sa wani reshe mai adalci ya fito daga zuriyar Dawuda, zai aikata gaskiya da adalci a ƙasar. 16A waɗannan kwanaki za a ceci mutanen Yahuza, mutanen Urushalima kuwa za su zauna lafiya. Sunan da za su sa wa Urushalima birninsu, shi ne, ‘Adalcinmu Ubangiji ne.’ 17#2Sam 7.12-16; 1Sar 2.4; 1Tar 17.11-14 Gama ni Ubangiji na ce Dawuda ba zai taɓa rasa mutumin da zai zauna a gadon sarautar Isra'ila ba. 18#L.Ƙid 3.5-10 Lawiyawa kuma ba za su rasa firistocin da za su tsaya a gabana, suna miƙa hadayun ƙonawa ba, da hadayu na gari na ƙonawa, su kuma miƙa sadaka har abada.”
19Ubangiji kuma ya yi magana da Irmiya ya ce, “Haka Ubangiji ya faɗa, 20idan ka iya hana dare da yini su bayyana a ƙayyadaddun lokatansu, 21to, ashe, alkawarin da na yi wa bawana Dawuda zai tashi ke nan, har ya rasa ɗan da zai yi mulki a gadon sarautarsa, alkawarin kuma da na yi wa firistoci masu yi mini hidima, da ma'aikatana, zai tashi. 22Kamar yadda ba a iya ƙidaya rundunan sammai ba, ba a iya kuma auna yashin teku ba, haka nan zan yawaita zuriyar bawana Dawuda da Lawiyawa, firistoci, masu yi mini hidima.”
23Ubangiji kuma ya ce wa Irmiya, 24“Ba ka ji abin da mutanen nan suke cewa ba? Wai, ‘Ubangiji ya ƙi iyalin nan biyu da ya zaɓa!’ Suka raina jama'ata, ba su kuma maishe ta al'umma ba. 25Amma ni Ubangiji na ce, idan ban kafa alkawarina game da yini, da kuma game da dare, da ka'idodin da take mulkin sammai da duniya ba, 26sa'an nan zan ƙi zuriyar Yakubu da bawana Dawuda. Ba kuma zan zaɓi wani daga cikin zuriyarsa ya yi mulkin zuriyar Ibrahim, da ta Ishaku, da ta Yakubu ba. Amma zan mayar musu da arzikinsu, in nuna jinƙai a kansu.”

Currently Selected:

Irm 33: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in