YouVersion Logo
Search Icon

Irm 32

32
Irmiya Ya Sayi Saura a Anatot
1 # 2Sar 25.1-7 Ubangiji ya yi magana da Irmiya a shekara ta goma ta mulkin Zadakiya, Sarkin Yahuza. A lokacin kuwa Nebukadnezzar yana da shekara goma sha takwas da sarauta a Babila. 2A lokacin nan kuwa sojojin Sarkin Babila sun kewaye Urushalima da yaƙi, annabi Irmiya kuwa yana a tsare a gidan waƙafi, a fādar Sarkin Yahuza. 3Zadakiya Sarkin Yahuza, ya sa shi a kurkuku, gama ya ce, “Don me kake yin annabci? Ka ce, Ubangiji ya ce, ga shi, zai ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa cinye shi da yaƙi. 4Zadakiya Sarkin Yahuza kuwa, ba zai tsere wa Kaldiyawa ba, amma za a ba da shi a hannun Sarkin Babila. Zai yi magana da shi fuska da fuska, ya kuma gan shi ido da ido. 5Sarkin Babila kuwa zai tafi da Zadakiya zuwa Babila. Zai zauna can sai lokacin da na ziyarce shi. Ko da ya yi yaƙi da Kaldiyawa ba zai yi nasara ba.”
6Irmiya ya ce, “Ubangiji ya yi magana da ni, cewa 7ga shi, Hanamel, ɗan Shallum kawuna, zai zo wurina ya ce mini, ‘Ka sayi gonata wadda take a Anatot, gama kai ne ka cancanci ka fanshe ta, sai ka saye ta.’ ” 8Sai Hanamel ɗan kawuna ya zo wurina a gidan waƙafi, bisa ga faɗar Ubangiji, ya ce mini, “Ka sayi gonata wadda take a Anatot a ƙasar Biliyaminu, gama kai ne ka cancanta ka mallake ta, kai ne za ka fanshe ta, sai ka saye ta.” Sa'an nan na sani wannan maganar Ubangiji ce. 9Sai na sayi gonar a Anatot daga hannun Hanamel ɗan kawuna, na biya shi shekel goma sha bakwai na azurfa. 10Na sa hannu a takarda, na buga hatimi na liƙe, na sami shaidu na kuwa auna kuɗin da ma'auni. 11Na ɗauki takardun ciniki waɗanda aka rubuta sharuɗan a ciki da wadda aka liƙe da wadda ba a liƙe ba, 12na ba Baruk, ɗan Neriya, ɗan Ma'aseya, a gaban Hanamel, ɗan kawuna, da gaban shaidun da suka sa hannun a takardar shaidar sayen, da gaban dukan Yahudawa waɗanda suke zaune a gidan waƙafi. 13Sai na umarci Baruk a gabansu cewa, 14“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Ka ɗauki waɗannan takardun shaida, wadda aka liƙe da wadda ba a liƙe ba, ka sa su a cikin tukunyar ƙasa domin kada su lalace.’ 15Gama haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa, ‘Gidaje, da gonaki, da gonakin inabi, za a sāke sayensu a ƙasan nan.’ ”
Addu'ar Irmiya
16Bayan da na ba Baruk, ɗan Neriya, takardar sharuɗan ciniki, sai na yi addu'a ga Ubangiji, na ce, 17“Ya Ubangiji Allah, kai ne ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka da ƙarfinka, ba abin da ya fi ƙarfinka. 18Kakan nuna madawwamiyar ƙauna ga dubbai, amma kakan hukunta wa 'ya'ya saboda laifin ubanninsu. Ya maigirma Maɗaukaki, Allah, sunanka kuwa Ubangiji Mai Runduna. 19Kai babban mashawarci ne, mai aikata manyan ayyukanka. Kana ganin dukan ayyukan 'yan adam. Kakan sāka wa kowa bisa ga halinsa da ayyukansa. 20Ka aikata alamu da al'ajabai a ƙasar Masar. Har wa yau kuma kana aikata su a Isra'ila da kuma cikin dukan al'ummai, ka yi wa kanka suna kamar yadda yake a yau. 21Ta wurin alamu da al'ajabai, da iko, da ƙarfi, da banrazana, ka fito da jama'arka Isra'ila daga ƙasar Masar. 22Ka kuwa ba su wannan ƙasa wadda ka rantse za ka ba kakanninsu. Ƙasar da take cike da yalwar albarka. 23Amma sa'ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.
24“Ga shi, Kaldiyawa sun gina mahaurai kewaye da birnin da suka kewaye shi da yaƙi. Saboda takobi, da yunwa, da annoba aka ba da birnin a hannun Kaldiyawa, waɗanda suke yaƙi da birnin. Abin da ka faɗa ya tabbata, ka kuwa gani. 25Duk da haka ya Ubangiji Allah, ka ce mini, ‘Sayi gonar da kuɗi, a gaban shaidu, ko da yake an ba da birnin a hannun Kaldiyawa.’ ”
26Ubangiji kuwa ya ce wa Irmiya, 27“Ni ne Ubangiji Allah na dukan 'yan adam, ba abin da ya fi ƙarfina. 28#2Sar 25.1-11; 2Tar 36.17-21 Saboda haka, ni Ubangiji, na ce zan ba da wannan birni a hannun Kaldiyawa da hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, za su ci birnin. 29Kaldiyawa da suke yaƙi da wannan birni za su zo, za su ƙone wannan birni da wuta ƙurmus, da gidaje waɗanda aka ƙona turare ga Ba'al a kan rufinsu. Aka kuma miƙa hadayu na sha ga gumaka, don su tsokane ni in yi fushi. 30Gama jama'ar Isra'ila da ta Yahuza, tun daga ƙuruciyarsu, ba su aikata kome a gabana ba sai mugunta, ba abin da jama'ar Isra'ila suka yi, sai tsokanata da gumaka don in yi fushi da ayyukan hannuwansu, ni Ubangiji na faɗa. 31Wannan birni ya tsokane ni ƙwarai tun lokacin da aka gina shi har zuwa yau, domin haka zan kawar da shi daga gabana. 32Wannan kuwa saboda muguntar jama'ar Isra'ila ce da ta Yahuza, wadda suka yi don su tsokane ni in yi fushi, su da sarakunansu, da shugabanninsu, da firistocinsu, da annabawansu, da mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima. 33Sun juya mini baya, ba su fuskance ni ba, ko da yake na yi ta koya musu, amma ba su saurara ga koyarwata ba. 34#2Sar 23.10; Irm 7.30,31; 19.1-6 Sun kafa gumakansu na banƙyama a cikin Haikalina wanda ake kira da sunana, sun kuwa ƙazantar da shi. 35#2Sar 23.10; Irm 7.31; L.Fir 18.21 Sun gina wa Ba'al masujadai a kwarin ɗan Hinnom don su miƙa 'ya'yansu mata da maza hadaya ga Molek, ni kuwa ban umarce su ba, ba shi kuwa a tunanina. Ga shi, sun aikata wannan abin banƙyama, don su sa Yahuza ta yi zunubi.”
Alkawari na Sa Zuciya
36“Domin haka ga abin da ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce a kan wannan birni wanda ka ce, ‘An ba da shi ga Sarkin Babila, da takobi, da yunwa, da annoba.’ 37Ga shi, zan tattaro su daga dukan ƙasashe inda na kora su, da fushina, da hasalata, da haushina. Zan komo da su a wannan wuri, zan sa su su zauna lafiya. 38Za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu. 39Zan ba su zuciya ɗaya, da tafarki ɗaya domin su yi tsorona har abada, domin amfanin kansu da na 'ya'yansu a bayansu. 40Zan yi madawwamin alkawari da su, ba zan fasa nuna musu alheri ba, zan kuwa sa tsorona a zukatansu domin kada su bar bina. 41Zan ji daɗin yi musu alheri. Zan dasa su a wannan ƙasa da aminci da zuciya ɗaya.”
42Gama haka Ubangiji ya faɗa, “Daidai kamar yadda na kawo wannan babbar masifa a kan jama'an nan, haka kuma zan kawo musu dukan waɗannan alherai da na alkawarta musu. 43Za a sayi gonaki a wannan ƙasa wadda kake cewa ta zama kufai, ba mutum, ba dabba a ciki, wadda aka ba da ita ga Kaldiyawa. 44Za a sayi gonaki da kuɗi, a sa hannu a kan sharuɗa, a hatimce su a gaban shaidu, a ƙasar Biliyaminu da wuraren da suke kewaye da Urushalima, da cikin garuruwan Yahuza, da na garuruwan ƙasar tudu, da a garuruwan kwaruruka, da a garuruwan Negeb, gama zan komar wa mutane da wadatarsu a ƙasarsu, ni Ubangiji na faɗa.”

Currently Selected:

Irm 32: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in