YouVersion Logo
Search Icon

Irm 34

34
Faɗaka ga Zadakiya
1 # 2Sar 25.1-11; 2Tar 36.17-21 Ubangiji ya yi magana da Irmiya sa'ad da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da dukan sojojinsa, da dukan sojojin mulkokin al'umman da suke a ƙarƙashinsa, da dukan mutane suke yaƙi da Urushalima da dukan biranenta. 2Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce wa Irmiya ya tafi, ya faɗa wa Zadakiya Sarkin Yahuza cewa, “Ni Ubangiji, zan ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa ƙone shi da wuta. 3Ba za ka tsere masa ba, amma lalle za a kama ka, a ba da kai a hannunsa. Za ka ga Sarkin Babila ido da ido, ka kuma yi magana da shi fuska da fuska. Za ka tafi Babila. 4Ya Zadakiya, Sarkin Yahuza, ka ji maganar da ni Ubangiji na faɗa a kanka, ba za ka mutu ta wurin takobi ba. 5Za ka mutu da salama. Kamar yadda aka ƙona wa sarakuna marigayanka turare, haka kai ma mutane za su ƙona maka turare, za su yi makoki dominka suna cewa, ‘Kaito, sarki ya rasu.’ Ni Ubangiji na faɗa.”
6Sai annabi Irmiya ya faɗa wa Zadakiya, Sarkin Yahuza, dukan maganan nan a Urushalima, 7sa'ad da sojojin Sarkin Babila suke yaƙi da Urushalima da kuma dukan biranen da suka ragu na Yahuza, wato Lakish da Azeka. Waɗannan su kaɗai ne biranen Yahuza masu garu da suka ragu.
Ta da Alkawari game da Bayin Ibraniyawa
8Ubangiji kuma ya yi magana da Irmiya bayan da Zadakiya ya yi alkawari da dukan mutanen Urushalima don a yi musu shelar ba da 'yanci, 9cewa kowa ya saki bayinsa, mata da maza, waɗanda suke Yahudawa. Kada kowa ya riƙe bawa wanda yake Bayahude, ɗan'uwansa. 10Sai suka yi biyayya. Dukan sarakuna da dukan jama'a waɗanda suka yi alkawarin, cewa kowa zai 'yantar da bawansa ko baiwarsa, ba za su ƙara bautar da su ba, suka yi biyayya, suka 'yantar da su. 11Daga baya kuwa suka sāke komo da waɗannan bayi, mata da maza waɗanda suka 'yantar, suka kuma mai da su bayi.
12Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce, 13“Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari da kakanninku lokacin da na fito da su daga ƙasar Masar daga bauta, na ce, 14#Fit 21.2; M.Sh 15.12 ‘A shekara ta bakwai, dole ne ku 'yantar da 'yan'uwanku, Ibraniyawa, waɗanda aka sayar muku, suka kuwa bauta muku shekara shida. Dole ne ku 'yantar da su daga bautarku.’ Amma kakanninku ba su kasa kunne gare ni ba. 15A 'yan kwanakin da suka wuce kuka yi abu mai kyau a gabana da kuka tuba, har kuka yi wa juna shelar 'yanci. Kuka yi alkawari a gabana a Haikalin da ake kira da sunana. 16Amma sai kuka sāke tunaninku, kuka ɓata sunana sa'ad da kowannenku ya komo da bayinsa, mata da maza, waɗanda kuka 'yantar, don su zauna yadda suke so. Ga shi kuma, kun komo da su su zama bayinku. 17Domin haka ni Ubangiji na ce, ba biyayya kuka yi mini ba, da irin shelar 'yancin da kowannenku ya yi wa ɗan'uwansa da maƙwabcinsa, saboda haka ni zan yi muku shelar 'yanci zuwa mutuwa ta takobi, da annoba, da yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya. 18Mutanen da suka keta alkawarina, ba su kuma kiyaye maganar alkawarin da suka yi a gabana ba, sa'ad da suka raba ɗan maraƙi kashi biyu, suka bi ta tsakiyarsa, 19wato manyan fādawan Yahuza, da na Urushalima, da 'yan majalisa, da firistoci da dukan jama'ar ƙasa, waɗanda suka bi ta tsakanin rababben ɗan maraƙin, 20zan bashe su a hannun abokan gabansu waɗanda suke neman ransu. Gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsaye da namomin jeji. 21Zadakiya, Sarkin Yahuza kuwa, da sarakunansa, zan bashe su a hannun abokan gābansu waɗanda suke neman ransu, wato sojojin Sarkin Babila, waɗanda suka tashi suka bar ku. 22Ni Ubangiji zan umarce su su komo zuwa wannan birni don su yi yaƙi da shi, su ci shi, su ƙone shi da wuta. Zan sa biranen Yahuza su zama kufai, ba masu zama a ciki.”

Currently Selected:

Irm 34: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in