Irm 22
22
1Haka Ubangiji ya faɗa, “Ka tafi ka gangara zuwa gidan Sarkin Yahuza, ka faɗi wannan magana a can, 2ka ce, ‘Ka ji maganar Ubangiji, ya Sarkin Yahuza, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda kai da barorinka, da mutanenka waɗanda suke shiga ta ƙofofin nan. 3Haka Ubangiji ya ce, ka yi gaskiya da adalci, ka ceci wanda ake masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka cuci baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, kada kuma ka zubar da jinin marasa laifi a wannan wuri. 4Hakika idan ka kiyaye wannan magana, sa'an nan sarakunan da za su zauna a kan gadon sarautar Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan gida da karusai da dawakai, su da barorinsu da jama'arsu. 5#Mat 23.28; Luk 13.35 Amma idan ba ka kula da waɗannan zantuttuka ba, na rantse da zatina,’ in ji Ubangiji, ‘wannan fāda ta zama kufai.’ ”
6Abin da Ubangiji ya ce ke nan a kan fādar Sarkin Yahuza,
“Kyanta kamar Gileyad take a gare
ni,
Kamar kuma ƙwanƙolin Lebanon.
Duk da haka zan maishe ta hamada,
Birnin da ba kowa ciki.
7Zan shirya waɗanda za su hallaka
ta.
Kowannensu da makamansa,
Za su sassare zaɓaɓɓun itatuwan
al'ul ɗinta, a jefa su a wuta.
8“Al'ummai masu yawa za su wuce ta gefen wannan birni, kowane mutum zai ce wa maƙwabcinsa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?’ 9Za su amsa, su ce, ‘Domin sun keta alkawarin Ubangiji Allahnsu, suka yi sujada ga gumaka, suka bauta musu.’ ”
10Ku mutanen Yahuza, kada ku yi
kuka saboda sarki Yosiya,
Kada ku yi makokin rasuwarsa,
Amma ku yi kuka ƙwarai saboda
ɗansa Yehowahaz.
Sun ɗauke shi, sun tafi da shi, ba zai
ƙara komowa ba,
Ba kuma zai ƙara ganin ƙasar da
aka haife shi ba.
11 #
2Sar 23.31-34; 2Tar 36.1-4 Gama haka Ubangiji ya ce a kan Yahowahaz, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, wanda ya gāji sarautar ubansa, Yosiya, wanda ya tafi ya bar wurin nan. Ba zai ƙara komowa nan ba. 12Amma a wurin da suka kai shi zaman talala, a can zai mutu, ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.
13Kaiton wanda ya gina gidansa ta
hanyar rashin adalci,
Benayensa kuma ta hanyar rashin
gaskiya.
Wanda ya sa maƙwabcinsa ya yi
masa aiki a banza,
Bai ba shi hakkinsa ba.
14Kaiton wanda ya ce,
“Zan gina wa kaina babban gida
Da waɗansu irin benaye
musamman.”
Ya yi masa tagogi,
Ya manna masa itacen al'ul,
Sa'an nan ya yi masa jan shafe.
15Kana tsammani kai sarki ne,
Da yake ƙasarka ta itacen al'ul
ce?
Amma ubanka ya ci, ya sha,
Ya yi gaskiya, ya aikata adalci,
Ya kuwa zauna lafiya.
16Ya biya wa matalauta da masu
bukata hakkinsu,
Ya kuwa yi kyau.
Abin da ake nufi da sanina ke nan,
In ji Ubangiji.
17Amma ka sa idonka da zuciyarka ga
ƙazamar riba,
Da zubar da jinin marar laifi,
Da yin zalunci da danniya.
18 #
2Sar 23.36—24.6; 2Tar 36.5-7 Domin haka ga abin da Ubangiji ya ce a kan Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza,
“Ba za su yi makoki dominsa ba, ko
su ce,
‘Wayyo ɗan'uwanmu!’ ko, ‘Wayyo
'yar'uwarmu!’
Ba za su yi makoki dominsa ba, su
ce,
‘Wayyo ubangidanmu!’ ko ‘Wayyo mai martaba!’
19Za a binne shi kamar jaki,
Za a ja shi a yar a bayan ƙofofin
Urushalima.”
20Ku haura zuwa Lebanon, ku yi
kuka,
Ku ta da muryarku cikin Bashan,
Ku yi kuka daga Abarim,
Gama an hallakar da dukan
ƙaunatattunku.
21Ubangiji ya yi muku magana a
lokacin wadatarku.
Amma kun ce, “Ba za mu kasa
kunne ba!”
Wannan shi ne halinku tun kuna
samari,
Don ba ku yi biyayya da murya
Ubangiji ba.
22Iska za ta kwashe shugabanninku,
Za a kai ƙaunatattunku cikin
bauta,
Sa'an nan za ku sha kunya ku ruɗe,
Saboda dukan muguntarku.
23Ya ku mazaunan Lebanon,
Waɗanda suke zaune cikin itatuwan
al'ul,
Irin nishin da za ku yi sa'ad da azaba
ta same ku,
Azaba ce irin ta mace mai
naƙuda!
24 #
2Sar 24.8-15; 2Tar 36.9,10 “Ni Ubangiji na rantse da raina, ko da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, zoben hatimi ne a yatsan hannun damana, duk da haka zan kwaɓe shi, 25in bashe shi a hannun waɗanda suke neman ransa, da a hannun wanda yake jin tsoronsa, wato Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da Kaldiyawa. 26Zan jefar da shi da uwarsa a wata ƙasa inda ba a haife shi ba, a can zai mutu. 27Amma ƙasan nan da suke marmarin komowa cikinta, ba za su koma cikinta ba.”
28Ashe, Yekoniya kamar fasasshen
tulu yake,
Wanda ba wanda ya kula da shi?
Me ya sa aka watsar da shi da
'ya'yansa,
A ƙasar da ba su sani ba?
29Ya ke ƙasa, ƙasa, ƙasa!
Ki ji maganar Ubangiji!
30Haka Ubangiji ya ce,
“Rubuta wannan mutum, marar
'ya'ya.
Mutumin da ba zai yi albarka a duk
kwanakinsa ba.
Gama ba wani daga zuriyarsa
Da zai gāji gadon sarautar Dawuda,
Ko ya yi mulki kuma a Yahuza.”
Currently Selected:
Irm 22: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979