Irm 21
21
An Yi Faɗi a kan Faɗuwar Urushalima
1Wannan ita ce maganar Ubangiji wadda ya faɗa wa Irmiya sa'ad da sarki Zadakiya ya aiki Fashur ɗan Malkiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma'aseya, wurin Irmiya cewa, 2#2Sar 25.1-11; 2Tar 36.17-21 “Ka tambayar mana Ubangiji, gama Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kawo mana yaƙi. Ko Ubangiji zai yi mana al'amuran nan nasa masu ban al'ajabi kamar yadda ya saba, ya sa Sarkin Babila ya janye, ya rabu da mu?”
3Sai Irmiya ya ce musu, 4“Ku faɗa wa Zadakiya, Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ga shi, zan juyo kayan yaƙin da suke hannunka waɗanda kake yaƙi da su gāba da Sarkin Babila, da sojojinsa, waɗanda suka kewaye garun birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan. 5Ni kaina zan yi yaƙi da kai da dukan ƙarfina, da hasalata, da dukan zafin fushina. 6Zan kuwa kashe mazaunan birnin nan, mutum da dabba, da babbar annoba. 7Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’
8“Sai ka faɗa wa wannan jama'a, ka ce, ‘Ni Ubangiji na ce, ga shi, na sa tafarkin rai da na mutuwa a gabanku. 9Shi wanda ya zauna a birnin nan zai mutu da takobi, da yunwa, da annoba, amma shi wanda ya fita ya ba da kansa ga Kaldiyawa waɗanda suke kewaye da ku zai rayu ya tserar da ransa. 10Gama na ƙudura zan kawo wa wannan birni masifa, ba alheri ba. Zan bashe shi a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai ƙone shi da wuta.’ ”
Annabci a kan Sarakunan Yahuza
11Are we “Sai ka faɗa wa gidan sarautar Yahuza cewa, ‘Ku ji maganar Ubangiji,
12“ ‘Ya gidan Dawuda, ni Ubangiji na ce,
Ku aikata adalci kowace safiya.
Ku ceci wanda aka yi masa ƙwace
daga hannun mai matsa masa,
Don kada hasalata ta tashi kamar
wuta,
Ta yi ƙuna, har ba mai iya kashe
ta,
Saboda mugayen ayyukanku.
13Ga shi, ina gāba da ku, ya ku
mazaunan kwarin,
Ya dutsen da yake a fili,’ in ji
Ubangiji.
‘Ku da kuke cewa, wa zai iya
gangarowa wurinku,
Ko kuwa wa zai shiga wurin
zamanku?
14Zan hukunta ku bisa ga ayyukanku,’
in ji Ubangiji,
‘Zan sa wa jejin ƙasar wuta.
Za ta cinye duk abin da yake kewaye da
ita.’ ”
Currently Selected:
Irm 21: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979