Kana tsammani kai sarki ne,
Da yake ƙasarka ta itacen al'ul
ce?
Amma ubanka ya ci, ya sha,
Ya yi gaskiya, ya aikata adalci,
Ya kuwa zauna lafiya.
Ya biya wa matalauta da masu
bukata hakkinsu,
Ya kuwa yi kyau.
Abin da ake nufi da sanina ke nan,
In ji Ubangiji.