“Sai ka faɗa wa wannan jama'a, ka ce, ‘Ni Ubangiji na ce, ga shi, na sa tafarkin rai da na mutuwa a gabanku. Shi wanda ya zauna a birnin nan zai mutu da takobi, da yunwa, da annoba, amma shi wanda ya fita ya ba da kansa ga Kaldiyawa waɗanda suke kewaye da ku zai rayu ya tserar da ransa.