YouVersion Logo
Search Icon

Irm 14

14
Babban Fari
1Maganar da Ubangiji ya yi wa Irmiya a kan fari ke nan,
2“Yahuza tana makoki,
Ƙofofin biranenta suna lalacewa,
Mutanenta suna kwance a ƙasa,
suna makoki,
Urushalima tana kuka da babbar
murya.
3Manyan mutanenta sun aiki
barorinsu su ɗebo ruwa.
Da suka je maɓuɓɓuga, sai suka
tarar ba ruwa.
Sai suka koma da tulunansu
haka nan,
An kunyatar da su, an ƙasƙantar
da su,
Suka lulluɓe kansu don kunya.
4Saboda ƙasar ta bushe,
Tun da ba a yi ruwa a kanta ba,
Manoma sun sha kunya,
Suka lulluɓe kansu don kunya.
5Barewa ma a saura takan gudu,
Ta bar ɗanta sabon haihuwa,
Domin ba ciyawa.
6Jakunan jeji suna tsaye a kan tuddan
da ba ciyawa,
Suna haki kamar diloli,
Idanunsu ba su gani
Domin ba abinci.”
7Irmiya ya ce,
“Ko da yake zunubanmu su ne
shaidunmu,
Ya Ubangiji, ka yi taimako saboda
sunanka!
Gama kāsawarmu ta yi yawa,
Domin mun yi maka zunubi.
8Ya kai, wanda kake begen Isra'ila,
Mai Cetonta a lokacin wahala,
Ƙaƙa ka zama kamar baƙo a ƙasar?
Kamar matafiyi wanda ya kafa
alfarwarsa a gefen hanya don ya
kwana, ya wuce?
9Ƙaƙa ka zama kamar wanda bai san
abin da zai yi ba,
Kamar jarumin da ya kasa yin
ceto?
Duk da haka, ya Ubangiji, kana nan
a tsakiyarmu.
Da sunanka ake kiranmu,
Kada ka bar mu!”
10Haka Ubangiji ya ce a kan waɗannan mutane, “Sun cika son yawaceyawace, ba su iya zama wuri ɗaya, don haka ni Ubangiji, ban yarda da su ba, zan tuna da laifofinsu in hukunta zunubansu.”
11Sai Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu'a domin lafiyar jama'an nan. 12Ko da sun yi azumi, ba zan ji kukansu ba, ko da sun miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta sha, ba zan karɓe su ba. Amma zan hallaka su da takobi, da yunwa, da annoba.”
13Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, ga shi, annabawa sun faɗa musu, sun ce, ‘Ba za ku ga takobi ko yunwa ba, amma zan ba ku dawwamammiyar salama a wannan wuri.’ ”
14Ubangiji kuwa ya ce mini, “Annabawa, annabcin ƙarya suka yi da sunana. Ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba, ban kuma yi magana da su ba. Annabcin da suke yi muku na wahayin ƙarya ne, dubar da suke yi marar amfani ce, tunaninsu ne kawai. 15Domin haka ga abin da ni Ubangiji na ce a kan annabawan da suke yin annabci da sunana, ko da yake ban aike su ba, waɗanda suke cewa, ‘Takobi da yunwa ba za su shigo ƙasan nan ba.’ Za a hallaka su da takobi da yunwa. 16Mutanen da suka yi wa annabci, za a jefar da su waje a kan titunan Urushalima, a karkashe su da yunwa da takobi, ba wanda zai binne su, da su, da matansu, da 'ya'yansu mata da maza. Zan sa muguntarsu ta koma kansu.
17“Irmiya, ka faɗa wa mutanen baƙin
ciki da ya same ka,
Ka ce, ‘Bari idanuna su yi ta zub da
hawaye dare da rana,
Kada su daina, saboda an buge
budurwa, 'yar jama'ata,
An yi mata babban rauni da dūka
mai tsanani.
18Idan na tafi cikin saura,
Sai in ga waɗanda aka kashe da
takobi!
Idan kuma na shiga birni,
Sai in ga waɗanda suke ta fama da
yunwa!
Gama annabi da firist, sai harkarsu
suke ta yi a ƙasar,
Amma ba su san abin da suke yi
ba.’ ”
Mutane Sun Roƙi Ubangiji
19“Ka ƙi Yahuza ke nan ɗungum?
Ranka kuma yana jin ƙyamar
Sihiyona ne?
Me ya sa ka buge mu, har da ba za
mu iya warkewa ba?
Mun zuba ido ga samun salama,
amma ba wani abin alheri da ya
zo.
Mun kuma sa zuciya ga warkewa,
amma sai ga razana.
20Mun san muguntar da muka yi, ya
Ubangiji,
Da wadda kakanninmu suka yi,
Gama mun yi maka zunubi.
21Saboda darajar sunanka, kada ka
wulakanta mu,
Kada kuma ka ƙasƙantar da
darajar kursiyinka,
Ka tuna da alkawarin da ka yi
mana,
Kada ka ta da shi.
22A cikin gumakan al'ummai akwai
mai iya sa a yi ruwa?
Sammai kuma su yi yayyafi?
Ashe, ba kai ne ba, ya Ubangiji
Allahnmu?
Domin haka a gare ka muke sa
zuciya,
Gama kai ne mai yin waɗannan
abubuwa duka.”

Currently Selected:

Irm 14: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in