YouVersion Logo
Search Icon

Irm 13

13
Misali da Abin Ɗamara
1Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, ya ce, “Tafi ka sayo lilin na yin ɗamara, ka sha ɗamara da shi kada kuwa ka tsoma shi a ruwa.” 2Sai na sayo abin ɗamara kamar yadda Ubangiji ya ce, na sha ɗamara da shi. 3Ubangiji kuma ya sāke yin magana da ni sau na biyu, 4ya ce, “Ka ɗauki abin ɗamara da ka sayo, wanda ka ɗaura, ka tafi Kogin Yufiretis, ka ɓoye shi a cikin kogon dutse.” 5Sai na tafi, na ɓoye shi a Yufiretis kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.
6Bayan an ɗan daɗe, sai Ubangiji ya ce mini, “Tashi, ka tafi Yufiretis, ka ɗauko abin ɗamara wanda na umarce ka ka ɓoye a can.” 7Sai na tafi Yufiretis, na haƙa na ɗauko abin ɗamara daga wurin da na ɓoye shi. Amma abin ɗamara ya lalace, ba shi da sauran amfani.
8Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 9“Haka zan lalatar da alfarmar Yahuza da yawan alfarmar Urushalima. 10Wannan muguwar jama'a, wadda ta ƙi jin maganata, wadda ta taurare, ta bi son zuciyarta, ta kuma bi gumaka ta bauta musu, ta yi musu sujada, za ta zama kamar abin ɗamaran nan, wanda ba shi da sauran amfani. 11Gama kamar yadda abin ɗamara yakan kame tam a gindin mutum, haka na sa dukan mutanen Isra'ila da dukan mutanen Yahuza su manne mini domin su zama jama'a, da suna, da yabo, da daraja a gare ni, amma sun ƙi ji.”
Misali da Tulun Ruwan Inabi
12“Sai ka faɗa musu wannan magana cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce, a cika kowane tulu da ruwan inabi.’ Su kuwa za su ce maka, sun sani sarai za a cika kowane tulu da ruwan inabi. 13Sa'an nan za ka faɗa musu, Ubangiji ya ce, ‘Ga shi, zan sa dukan mazaunan ƙasar su bugu da ruwan inabi, wato sarakunan da suka hau gadon sarautar Dawuda, da firistoci, da annabawa, da dukan mazaunan Urushalima. 14Zan sa su kara da junansu, iyaye maza da 'ya'yansu maza, in ji Ubangiji. Tausayi, ko juyayi, ko jinƙai ba za su sa in fasa hallaka su duka ba.’ ”
Yahuza bai Tuba ba, za a Kai shi Zaman Talala
15Ku kasa kunne, ku ji,
Kada ku yi girmankai, gama
Ubangiji ya yi magana.
16Ku girmama Ubangiji Allahnku,
Kafin ya kawo duhu,
Kafin kuma ƙafafunku su yi tuntuɓe
a kan dutse, da duhu duhu,
Sa'ad da kuke neman haske, sai ya
maishe shi duhu,
Ya maishe shi duhu baƙi ƙirin.
17Amma idan ba za ku ji ba,
Raina zai yi kuka a ɓoye saboda
girmankanku,
Idanuna za su yi kuka ƙwarai, za su
zub da hawaye,
Domin an kai garken Ubangiji zuwa
bauta.
18Ubangiji ya ce wa Irmiya,
“Ka faɗa wa sarki da sarauniya,
uwarsa, su sauka daga gadon
sarautarsu,
Domin an tuɓe kyakkyawan rawanin
sarautarsu daga kansu.
19An kulle biranen Negeb,
Ba wanda zai buɗe su,
Yahuza duka an kai ta zaman dole,
Dukanta an kai ta zaman dole.
20“Ku ta da idanunku, ku ga waɗanda
suke zuwa daga arewa!
Ina kyakkyawan garken nan da aka
ba ku?
21Me za ku ce sa'ad da aka naɗa muku
shugabanni,
Waɗanda ku da kanku kuka koya
musu, suka zama abokanku?
Ashe, azabai ba za su auko muku ba
Kamar yadda sukan auko wa mace
mai naƙuda?
22Idan kun ce a zuciyarku,
‘Me ya sa waɗannan abubuwa suka
same mu?’
Saboda yawan zunubanku ne,
Shi ya sa an tone tsiraicinku,
Aka wahalshe ku.
23Mutumin Habasha zai iya sāke
launin fatar jikinsa?
Ko kuwa damisa za ta iya sāke
dabbare-dabbarenta?
Idan haka ne, ku kuma za ku iya yin
nagarta,
Ku da kuka saba da yin mugunta.
24Zan warwatsar da ku
Kamar yadda iskar hamada take
watsar da ƙaiƙayi.”
25Ubangiji ya ce, “Wannan shi ne
rabonku,
Rabon da na auna muku, ni Ubangiji
na faɗa.
Domin kun manta da ni, kun dogara
ga ƙarairayi,
26Ni kaina kuma zan kware muku
suturarku ta rufe fuskarku
Don a ga tsiraicinku.
27Na ga abubuwanku masu
banƙyama,
Wato zinace-zinacenku, da haniniya
kamar dawakai,
Da muguwar sha'awarku ta
karuwanci a kan tuddai da filaye,
Ya Urushalima, taki ta ƙare!
Har yaushe za a tsarkake ki?”

Currently Selected:

Irm 13: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in