YouVersion Logo
Search Icon

Irm 15

15
Fushin Ubangiji da Yahuza bai Huce Ba
1 # Fit 32.11-14; L.Ƙid 14.13-19; 1Sam 7.5-9 Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da a ce Musa da Sama'ila za su tsaya a gabana, duk da haka zuciyata ba za ta komo wurin mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana su yi tafiyarsu! 2#W.Yah 13.10 Sa'ad da suka tambaye ka, ‘Ina za mu tafi?’ Sai ka faɗa musu cewa, Ubangiji ya ce,
“Waɗanda suke na annoba, su tafi ga
annoba!
Waɗanda suke na takobi, su tafi ga
takobi!
Waɗanda suke na yunwa, su tafi ga
yunwa!
Waɗanda suke na bauta, su tafi ga
bauta!”
3Zan sa musu masu hallakarwa huɗu, in ji Ubangiji, “da takobi don kisa, da karnuka don yayyagawa, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobin duniya don su cinye, su hallakar. 4#2Sar 21.1-16; 2Tar 33.1-9 Zan kuma sa su zama abin banƙyama ga dukan mulkokin duniya saboda abin da Manassa ɗan Hezekiya, Sarkin Yahuza ya aikata a Urushalima.
5“Wa zai ji tausayinki, ya
Urushalima?
Wa zai yi baƙin ciki dominki?
Wa kuma zai ratso wurinki don ya
tambayi lafiyarki?
6Ni Ubangiji na ce, kun ƙi ni, kuna ta
komawa da baya,
Don haka na nuna ikona gāba da ku,
na hallaka ku,
Na gaji da jin tausayinku!
7Na sheƙe su da abin sheƙewa a
ƙofofin garuruwan ƙasar.
Na sa 'ya'yansu su mutu, na hallaka
mutanena,
Ba su daina yin mugayen ayyukansu
ba.
8Na yawaita gwauraye, wato mata da
mazansu suka mutu,
Fiye da yashin teku.
Na kawo wa uwayen samari mai
hallakarwa da tsakar rana.
Na sa azaba da razana su auka musu
farat ɗaya.
9Ita wadda ta haifi 'ya'ya bakwai ta
yi yaushi ta suma,
Ranarta ta faɗi tun lokaci bai yi ba,
An kunyatar da ita, an wulakantar
da ita.
Waɗanda suka ragu daga cikinsu
Zan bashe su ga takobi gaban abokan
gābansu.
Ni Ubangiji na faɗa.”
10Kaitona, ya mahaifiyata, da kika haife ni, mai jayayya mai gardama da kowa cikin dukan ƙasar! Ban ba da rance ba, ba kuma wanda ya ba ni rance, duk da haka dukansu suna zagina. 11Ubangiji ya ce mini, “Zan keɓe ka domin alheri, hakika zan sa abokan gaba su yi roƙo gare ka a lokacin bala'i da kuma lokacin damuwa. 12Wa zai iya karya ƙarfe ko tagulla daga arewa?”
13Ubangiji ya ce mini, “Zan ba da wadatarku da dukiyarku ganima kyauta, saboda dukan zunubanku a dukan ƙasar. 14Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama fushina ya kama kamar wuta, zai yi ta ci har abada.”
15Sa'an nan Irmiya ya ce, “Ya
Ubangiji, ka sani.
Kai ne, ka ziyarce ni,
Ka kuma sāka wa waɗanda suke
tsananta mini.
Ka sani saboda kai nake shan zargi.
16Maganarka da na samu na ci.
Maganarka kuwa ta zama abar
murna a gare ni,
Ta faranta mini zuciya.
Gama ana kirana da sunanka,
Ya Ubangiji Allah Mai Runduna.
17Ban zauna cikin ƙungiyar masu
annashuwa ba.
Ban kuwa yi murna ba,
Na zauna ni kaɗai saboda kana tare
da ni,
Gama ka sa na cika da haushi.
18Me ya sa azabata ta ƙi ƙarewa,
Raunukana kuma ba su warkuwa,
Sun kuwa ƙi warkewa?
Za ka yaudare ni kamar rafi,
Ko kamar ruwa mai ƙafewa?”
19“Domin haka ga abin da ni, Ubangiji
na ce,
Idan ka komo sa'an nan zan kawo
ka.
Za ka tsaya a gabana.
Idan ka hurta abin da yake gaskiya
ba na ƙarya ba,
Za ka zama kakakina.
Za su komo gare ka,
Amma kai ba za ka koma wurinsu
ba.
20Zan maishe ka garun tagulla saboda
waɗannan mutane,
Za su yi yaƙi da kai, amma ba za
su yi nasara a kanka ba,
Gama ina tare da kai don in cece ka,
in kuɓutar da kai.
21Zan kuɓutar da kai daga hannun
mugaye,
Zan ɓamɓare ka daga hannun
marasa tausayi.”

Currently Selected:

Irm 15: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in