YouVersion Logo
Search Icon

L.Mah 11

11
Yefta ya Ceci Isra'ilawa daga Hannun Ammonawa
1Yefta mutumin Gileyad ne, shi kuwa jarumi ne, amma mahaifiyarsa karuwa ce. Gileyad ne mahaifinsa. 2Matar Gileyad ta haifa masa 'ya'ya maza. Sa'ad da suka yi girma, sai suka kori Yefta, suka ce masa, “Ba za ka ci gādo a gidan mahaifinmu ba, gama kai ɗan wata mace ne.” 3Sai Yefta ya gudu daga wurin 'yan'uwansa, ya zauna a ƙasar Tob. 'Yan iska kuwa suka taru wurin Yefta, sukan tafi yawo tare da shi.
4Ana nan sai Ammonawa suka kai wa Isra'ilawa yaƙi. 5Da haka ta auku, sai shugabannin Gileyad suka tafi su komo da Yefta daga ƙasar Tob. 6Suka ce wa Yefta, “Ka zo, ka zama shugabanmu don mu yi yaƙi da Ammonawa.”
7Amma Yefta ya ce wa dattawan Gileyad, “Ba ku kuka ƙi ni, kuka kore ni daga gidan mahaifina ba? Me ya sa kuka zo wurina a lokacina da kuke shan wahala?”
8Sai dattawan Gileyad suka amsa masa, “Abin da ya sa muka zo wurinka yanzu, shi ne domin ka tafi tare da mu ne mu yi yaƙi da Ammonawa, ka kuma zama shugaban dukan jama'ar Gileyad.”
9Yefta kuwa ya ce musu, “Idan kuka koma da ni gida domin in yi yaƙi da Ammonawa, idan Ubangiji ya ba da su a hannuna, to, zan zama shugabanku.”
10Suka amsa suka ce wa Yefta, “Ubangiji shi ne shaida tsakaninmu, lalle za mu yi maka kamar yadda ka ce.” 11Yefta kuwa ya tafi tare da dattawa Gileyad. Su kuwa suka naɗa shi shugabansu da sarkin yaƙinsu. Yefta kuwa ya faɗi dukan abin da yake zuciyarsa a gaban Ubangiji a Mizfa.
12Yefta kuwa ya aiki jakadu wurin Sarkin Ammonawa da cewa, “Me ya haɗa ka da ni, da ka zo ƙasata da yaƙi?”
13Sarkin Ammonawa ya amsa wa jakadun Yefta cewa, “Domin lokacin da Isra'ilawa suna tahowa daga Masar sun ƙwace mini ƙasa tun daga Kogin Arnon zuwa Kogin Yabbok, har zuwa Kogin Urdun. Yanzu sai ka mayar mini da ita cikin lumana.”
14Yefta kuma ya sāke aike da jakadu wurin Sarkin Ammonawa, 15tare da amsa, ya ce, “Isra'ilawa ba su ƙwace ƙasar Mowab ko ta Ammonawa ba. 16Amma sa'ad da suka baro Masar, sun bi ta jeji zuwa Bahar Maliya, suka zo Kadesh. 17#L.Ƙid 20.14-21 Sa'an nan suka aike da jakadu wurin Sarkin Edom, su roƙe shi ya bar su su wuce ta ƙasarsa. Amma Sarkin Edom bai yarda ba. Suka kuma aika wa Sarkin Mowab, shi ma bai yarda ba, don haka Isra'ilawa suka zauna a Kadesh.
18 # L.Ƙid 21.4 “Sa'an nan suka ci gaba da tafiya ta cikin hamada. Suka zaga ƙasar Edom da ta Mowab. Da suka kai gabashin ƙasar Mowab, sai suka yi zango a bakin Kogin Arnon, amma ba su haye kogin ba, gama shi ne iyakar ƙasar Mowab. 19#L.Ƙid 21.21-24 Sa'an nan Isra'ilawa suka aike da jakadu wurin Sihon Sarkin Heshbon ta Amoriyawa, suka roƙe shi, suka ce, ‘Ka yarda mana mu wuce ta ƙasarka.’ 20Amma Sihon bai amince wa Isra'ilawa su bi ta ƙasarsa, su wuce ba. Ya kuwa tattara mutanensa, ya kafa sansaninsa a Yahaza, ya yi yaƙi da Isra'ilawa. 21Ubangiji Allah na Isra'ila kuwa ya ba da Sihon da mutanensa duka ga Isra'ilawa, suka ci su da yaƙi. Suka kuwa mallaki dukan ƙasar Amoriyawa da mazaunan ƙasar. 22Suka mallaki dukan ƙasar Amoriyawa tun daga Kogin Arnon har zuwa Kogin Yabbok, tun kuma daga jeji zuwa Kogin Urdun. 23To, ai, ka ga Ubangiji Allah na Isra'ila ne ya kori Amoriyawa saboda jama'ar Isra'ila. To, yanzu so kake ka ƙwace mana? 24Kai ba za ka mallaki abin da Kemosh, allahnka, ya ba ka mallaka ba? Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya mallakar mana, za mu mallake shi. 25#L.Ƙid 22.1-6 Kana zaton ka fi Balak, ɗan Ziffor, Sarkin Mowab? Ka ji ya taɓa hamayya da Isra'ilawa? Ko kuwa ka ji ya taɓa yin yaƙi da su? 26Shekara ɗari uku Isra'ilawa suka yi zamansu a Heshbon da ƙauyukanta, da Arower da ƙauyukanta, da dukan biranen da suke a gefen Kogin Arnon, me ya sa ba ka ƙwace su tun a wancan lokaci ba? 27Don haka ni ban yi maka laifi ba, kai ne kake yi mini laifi da kake yaƙi da ni. Ubangiji ne alƙali yau, zai shara'anta tsakanin Isra'ilawa da Ammonawa.” 28Amma Sarkin Ammonawa bai kula da saƙon da Yefta ya aika masa ba.
29Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko wa Yefta, sai ya tashi ratsa Gileyad da Manassa zuwa Mizfa ta Gileyad, daga can ya haura zuwa wurin Ammonawa. 30Yefta kuwa ya yi wa'adi ga Ubangiji, ya ce, “Idan dai ka ba da Ammonawa a hannuna, 31duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don ya tarye ni, sa'ad da na komo daga yaƙin Ammonawa da nasara, zai zama na Ubangiji, zan kuwa miƙa shi hadaya ta ƙonawa.” 32Yefta ya haye zuwa wurin Ammonawa domin ya yi yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannunsa. 33Ya karkashe su da mummunan kisa tun daga Arower zuwa yankin Minnit, har zuwa Abel-keramim. Ya cinye biranensu guda ashirin. Da haka Ammonawa suka sha kāshi a hannun Isra'ilawa.
'Yar Yefta
34Da Yefta ya koma gidansa a Mizfa, sai ga 'yarsa, tilo ta fito da kiɗa da rawa don ta tarye shi. Ita ce kaɗai 'yarsa, banda ita ba shi da ɗa ko 'ya. 35#L.Ƙid 30.2 Sa'ad da ya gan ta sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Kaito, 'yata, kin karya mini gwiwa, kin zamar mini babban dalilin wahala. Na riga na yi wa'adi ga Ubangiji, ba kuwa zan iya warware shi ba.”
36Sai ta ce masa, “Baba, idan ka riga ka yi wa'adi ga Ubangiji, sai ka yi da ni bisa ga wa'adinka, da yake Ubangiji ya ɗau maka fansa a kan Ammonawa, abokan gābanka.” 37Ta kuma ce masa, “Ina so ka yardar mini in tafi kan duwatsu ni da ƙawayena in yi makokin budurcina har wata biyu.”
38Sai ya ce mata, “Tafi.” Ya sallame ta, ta tafi har wata biyu ɗin. Ita da ƙawayenta kuwa suka yi makokin budurcinta a kan duwatsu. 39Bayan wata biyu, sai ta koma wurin mahaifinta, shi kuwa ya yi abin da ya yi wa Ubangiji wa'adi. Ta rasu ba ta taɓa sanin namiji ba. Wannan kuwa ya zama al'ada a cikin Isra'ila, 40wato matan Isra'ilawa sukan fita kowace shekara su yi makoki kwana huɗu don 'yar Yefta, mutumin Gileyad.

Currently Selected:

L.Mah 11: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

Video for L.Mah 11