L.Mah 10
10
Tola da Yayir Sun Shugabanci Isra'ilawa
1Bayan mutuwar Abimelek, sai Tola, ɗan Fuwa, ɗan Dodo, daga kabilar Issaka ya tashi don ya ceci Isra'ilawa. Ya zauna a Shamir, a ƙasar tuddai ta Ifraimu. 2Ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin da uku, sa'an nan ya rasu. Aka binne shi a Shamir.
3Bayansa kuma sai Yayir mutumin Gileyad, ya tashi ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin da biyu. 4Yana da 'ya'ya maza guda talatin, waɗanda suke hawan jakai talatin. Suna kuma da birane talatin a ƙasar Gileyad, waɗanda har yanzu ake kira biranen alfarwai. Ana kiran biranen Hawwot-Yayir, wato na Yayir. 5Yayir ya rasu aka binne shi a Kamon.
Ammonawa Sun Matsa wa Isra'ilawa
6Isra'ilawa suka sāke yi wa Ubangiji zunubi. Suka yi sujada ga Ba'al da Ashtarot, allolin Suriyawa, da na Sidon, da na Mowab, da na Ammonawa, da na Filistiyawa. Suka bar bin Ubangiji, suka daina yi masa sujada. 7Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa, ya ba da su ga Filistiyawa, da Ammonawa. 8Suka murƙushe Isra'ilawa, suka matsa musu. Har shekara goma sha takwas suka yi ta matsa dukan Isra'ilawan da suke a hayin Urdun daga gabas, a cikin Gileyad, inda Amoriyawa suke zaune. 9Ammonawa kuma suka haye Urdun don su yaƙi mutanen Yahuza, da na Biliyaminu, da na kabilar Ifraimu. Isra'ilawa kuwa suka matsu ƙwarai.
10Sa'an nan Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suna cewa, “Mun yi maka zunubi, gama mun bar binka, ya Allahnmu, muka yi wa Ba'al sujada.”
11Ubangiji ya amsa musu, ya ce, “Ban cece ku daga hannun Masarawa, da Amoriyawa, da Ammonawa, da Filistiyawa, 12da Sidoniyawa, da Amalekawa, da Mawonawa ba, wato su da suka matsa muku a dā, ku kuma kuka yi kuka gare ni? 13Amma duk da haka kuka bar bina, kuka yi sujada ga waɗansu alloli, don haka ni kuma ba zan ƙara cetonku ba. 14Tafi, ku yi wa allolin da kuka zaɓa kuka, don su cece ku a lokacin wahalarku.”
15Amma Isra'ilawa suka ce wa Ubangiji, “Mun yi zunubi, ka yi mana duk irin abin da ka ga dama, amma in ka yarda ka cece mu yau.” 16Sa'an nan suka zubar da gumakan da suke wurinsu, suka yi wa Ubangiji sujada. Shi kuwa ya damu saboda azabar da Isra'ilawa suke sha.
17Sojojin Ammonawa kuwa, suka tattaru, suka kafa sansani a Gileyad. Isra'ilawa kuma suka tattaru, suka kafa nasu sansani a Mizfa. 18Shugabanni da mutanen Gileyad suka ce wa junansu. “Wa zai fara yaƙi da Ammonawa? Shi zai zama shugaban duk wanda yake Gileyad.”
Currently Selected:
L.Mah 10: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979