Yefta kuwa ya yi wa'adi ga Ubangiji, ya ce, “Idan dai ka ba da Ammonawa a hannuna, duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don ya tarye ni, sa'ad da na komo daga yaƙin Ammonawa da nasara, zai zama na Ubangiji, zan kuwa miƙa shi hadaya ta ƙonawa.”