Yak 4
4
Abuta da Duniya
1Me yake haddasa gāba da husuma a tsakaninku? Ashe, ba sha'awace-sha'awacenku ne suke yaƙi da juna a zukatanku ba? 2Kukan yi marmarin abu ku rasa, sai ku yi kisankai. Kukan yi kwaɗayi, ku kasa samu, sai ku yi husuma da faɗa. Kukan rasa don ba kwa addu'a ne. 3Kukan yi addu'a ku rasa, don kun yi ta da mugun nufi ne, don ku ɓatar a kan nishaɗinku.
4Maciya amana! Ashe, ba ku sani abuta da duniya gāba ce da Allah ba? Saboda haka, duk mai son abuta da duniya, yā mai da kansa mai gāba da Allah ke nan. 5Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce, “Wannan ruhu da Allah ya sa a cikinmu yana tsaronmu ƙwarai”? 6#K.Mag 3.34 Allah shi yake yin mayalwacin alheri. Domin haka Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana yi wa masu tawali'u alheri.” 7Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah, ku yi tsayayya da Iblis, lalle kuwa zai guje muku. 8Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku. Ku tsarkake al'amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukattanku, ya ku masu zuciya biyu. 9Ku yi nadama, ku yi baƙin ciki, ku yi ta kuka. Dariyarku tă zama baƙin ciki, murnarku tă koma ɓacin zuciya. 10Ku ƙasƙantar da kanku ga Ubangiji, shi kuwa zai ɗaukaka ku.
Ɗora wa Ɗan'uwa Laifi
11Ya ku 'yan'uwana, kada ku kushe wa juna. Kowa ya kushe wa ɗan'uwansa, ko ya ɗora masa laifi, ya kushe wa shari'a ke nan, ya kuma ɗora mata laifi. In kuwa ka ɗora wa shari'a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne. 12Mai ba da Shari'a ɗaya ne, shi ne kuma mai yinta, shi ne kuwa mai ikon ceto da hallakarwa. To, kai wane ne har da za ka ɗora wa ɗan'uwanka laifi?
Kada a Yi Fariya Saboda Gobe
13 #
K.Mag 27.1
To, ina masu cewa, “Yau ko gobe za mu je gari kaza, mu shekara a can, mu yi ta ciniki, mu ci riba”? 14Alhali kuwa ba ku san abin da gobe za ta kawo ba. Wane iri ne ranku? Ai, kamar hazo yake, jim kaɗan sai ya ɓace. 15Sai dai ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya nufa, ya kai rai, ma yi kaza da kaza.” 16Amma ga shi, kuna fariya ta alfarmar banza da kuke yi. Duk irin wannan fariya kuwa muguwar aba ce. 17Saboda haka, duk wanda ya san abin da ya kamata, ya kuwa kasa yi, ya yi zunubi ke nan.
Currently Selected:
Yak 4: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979