Yak 3
3
Ɓarnar Harshe
1Ya ku 'yan'uwana, kada yawancinku su zama masu koyarwa, domin kun sani, mu da muke koyarwa za a yi mana shari'a da ƙididdiga mafi tsanani. 2Domin dukanmu muna yin kuskure da yawa. In kuwa mutum ba ya shirme a maganarsa, to, shi cikakken mutum ne, yana kuwa iya kame duk sauran gaɓoɓinsa ma. 3Ga misali, idan mun sa linzami a bakin doki, don mu bi da shi, mukan sarrafa dukan jikinsa ma. 4Ku dubi jiragen ruwa kuma, ko da yake suna da girma haka ƙaƙƙarfar iska kuma tana kora su, duk da haka, da ɗan ƙaramin ƙarfe ne matuƙi yake juya su duk inda ya nufa. 5Haka ma harshe yake, ga shi, ɗan ƙaramin abu ne, sai manyan fariya! Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake kunna wa babban jeji wuta!
6Harshe ma wuta ne fa! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata dukan jiki, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa Gidan Wuta ne yake zuga shi. 7Don kuwa ana iya sarrafa kowace irin dabba, da tsuntsu, da masu jan ciki, da halittar ruwa, ɗan adam har yā sarrafa su ma, 8amma ba ɗan adam ɗin da zai iya sarrafa harshe, ai, mugunta ne da ba ta hanuwa, a cike yake da dafi mai kashewa. 9#Far 1.26 Da shi muke yabon Ubangiji Uba, da shi kuma muke zagin mutane waɗanda aka halitta da kamannin Allah. 10Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba! 11Ashe, marmaro ɗaya ya iya ɓuɓɓugowa da ruwan daɗi da na zartsi ta ido guda? 12Ya 'yan'uwana, ashe, ɓaure yana iya haifar zaitun? Ko kuwa inabi ya haifi ɓaure? Haka kuma, ba dama a sami ruwan daɗi a idon ruwan zartsi.
Hikima Mai Saukowa daga Sama
13Ina mai hikima da fahimi a cikinku? To, ta kyakkyawan zamansa sai ya nuna aikinsa da halin tawali'u da hikima suke sawa. 14Amma in kuna da matsanancin kishi da sonkai a zuciyarku, kada ku yi alwashi da haka, kuna saɓa wa gaskiya. 15Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga Sama ba ce, ta duniya ce, ta son zuciya, ta Shaiɗan kuma. 16A duk inda kishi da sonkai suke, a nan hargitsi da kowane irin mugun aiki ma suke. 17Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma. 18Daga irin salama wanda masu sulhuntawa suke shukawa akan girbe adalci.
Currently Selected:
Yak 3: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979