1
Yak 4:7
Littafi Mai Tsarki
HAU
Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah, ku yi tsayayya da Iblis, lalle kuwa zai guje muku.
Compare
Explore Yak 4:7
2
Yak 4:8
Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku. Ku tsarkake al'amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukattanku, ya ku masu zuciya biyu.
Explore Yak 4:8
3
Yak 4:10
Ku ƙasƙantar da kanku ga Ubangiji, shi kuwa zai ɗaukaka ku.
Explore Yak 4:10
4
Yak 4:6
Allah shi yake yin mayalwacin alheri. Domin haka Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana yi wa masu tawali'u alheri.”
Explore Yak 4:6
5
Yak 4:17
Saboda haka, duk wanda ya san abin da ya kamata, ya kuwa kasa yi, ya yi zunubi ke nan.
Explore Yak 4:17
6
Yak 4:3
Kukan yi addu'a ku rasa, don kun yi ta da mugun nufi ne, don ku ɓatar a kan nishaɗinku.
Explore Yak 4:3
7
Yak 4:4
Maciya amana! Ashe, ba ku sani abuta da duniya gāba ce da Allah ba? Saboda haka, duk mai son abuta da duniya, yā mai da kansa mai gāba da Allah ke nan.
Explore Yak 4:4
8
Yak 4:14
Alhali kuwa ba ku san abin da gobe za ta kawo ba. Wane iri ne ranku? Ai, kamar hazo yake, jim kaɗan sai ya ɓace.
Explore Yak 4:14
Home
Bible
Plans
Videos