Ish 55
55
Allah Ya Nuna Jinƙai ga Kowa
1 #
W.Yah 21.6; 22.17 Ubangiji ya ce,
“Duk mai jin ƙishi ya zo,
Ga ruwa a nan!
Ku da ba ku da kuɗi ku zo,
Ku sayi hatsi ku ci!
Ku zo ku sayi ruwan inabi da madara,
Ba za ku biya kome ba!
2Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba?
Don me za ku ɓad da albashinku, amma kuna ta shan yunwa?
Ku kasa kunne gare ni, ku yi abin da na faɗa,
Za ku sha daɗin abinci mafi kyau duka.
3 #
A.M 13.34
“Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni,
Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai!
Zan yi tabbataccen alkawari da ku,
Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.
4Na sa ya zama shugaba, da shugaban yaƙi na al'ummai,
Ta wurinsa kuwa na nuna musu girmana.
5Yanzu kuwa za ku kira al'ummai, baƙi,
Dā ba su kuwa san ku ba, ko da rana ɗaya,
Amma yanzu za su sheƙo a guje domin su haɗa kai da ku!
Ni, Ubangiji Allahnku, Allah Mai Tsarki na Isra'ila,
Zan sa dukan wannan ya faru,
Zan ba ku girma da daraja.”
6Ku juyo wurin Ubangiji, ku yi addu'a gare shi,
Yanzu da yake kusa.
7Bari mugaye su bar irin al'amuransu,
Su sāke irin tunaninsu.
Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu,
Shi mai jinƙai ne, mai saurin gafartawa.
8Ubangiji ya ce,
“Tunanina ba kamar irin naku ba ne,
Al'amurana kuma dabam suke da naku.
9Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa,
Haka al'amurana da tunanina suke nesa da naku.
10 #
2Kor 9.10
“Maganata kamar dusar ƙanƙara take,
Kamar kuma ruwan sama da yake saukowa domin ya jiƙe duniya.
Ba za su kasa sa amfanin gona ya yi girma ba,
Sukan ba da iri domin shukawa, da abinci kuma domin a ci.
11To, haka maganar da na faɗa take,
Ba ta kāsa cika abin da na shirya mata,
Za ta yi kowane abin da na aike ta ta yi.
12“Za ku fita daga cikin Babila da murna,
Za a bi da ku, ku fita daga birnin da salama.
Duwatsu da tuddai za su ɓarke da waƙa,
Itatuwa za su yi ta sowa don murna!
13Itacen fir zai tsiro a wurin da sarƙaƙƙiya take yanzu,
Itacen ci-zaƙi zai tsiro a maimakon ƙayayuwa.
Wannan zai zama alamar da za ta kasance har abada,
Matuni ne na abin da ni, Ubangiji, na yi.”
Currently Selected:
Ish 55: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979