YouVersion Logo
Search Icon

Ish 56

56
Sakamakon Cikar Alkawarin Ubangiji
1Ga jawabin da Ubangiji ya yi, “Ku kiyaye gaskiya ku yi adalci, gama cetona yana zuwa nan da nan, za a kuwa bayyana adalcina. 2Mai albarka ne mutumin da yake aikata wannan, da ɗan adam da yake riƙe da shi kam, wanda yake kiyaye ranar Asabar, bai kuwa ƙazantar da ita ba, wanda kuma ya tsame hannunsa daga aikata kowace irin mugunta.”
3Kada baƙon da ya hada kansa da mutanen Ubangiji ya ce, hakika Ubangiji zai ware shi daga jama'arsa.
Kada kuma baban ya ce shi busasshen itace ne. 4Ga abin da Ubangiji ya ce, wa mutanen nan, “Ku babani waɗanda kuka kiyaye Asabar ɗina, ku da kuka zaɓi abubuwan da suka gamshe ni, kuka kuwa cika alkawarina da aminci, 5zan ba ku matuni da suna a Haikalina da cikin garukana, da sun fi na 'ya'ya mata da maza. Zan ba ku tabbataccen suna wanda ba za a raba ku da shi ba.”
6Ubangiji ya ce wa baƙin da suka bi shi, don su yi masa hidima, suna ƙaunar sunansa, sun kuma zama bayinsa, dukan wanda yake kiyaye ranar Asabar, bai kuwa ɓata ta ba, ya kuma cika alkawarinsa da aminci, 7#Mat 21.13; Mar 11.17; Luk 19.46 “Zan kai ku tsattsarkan dutsena, in sa ku yi murna a masujadata. Hadayunku na ƙonawa da sadakokinku za su zama abin karɓa a bagadena. Za a kira Haikalina wurin yin addu'a na dukan jama'a.”
8Haka Ubangiji Allah, shi wanda ya tattara Isra'ilawa korarru, ya faɗa, ya ce, “Zan ƙara tattaro waɗansu, bayan waɗanda na riga na tattara.”
Kā da Tsafin Isra'ila
9Dukanku namomin jeji ku zo ku ci, dukanku namomin jeji. 10Matsaransa makafi ne, dukansu marasa ilimi ne. Dukansu kamar karnuka ne bebaye, ba su iya haushi ba, suna kwance suna ta mafarki, suna jin daɗin rurumi! 11Suna kama da karnuka masu zarin ci, ba su taɓa samun abin da ya ishe su ba. Makiyayan nan kuma ba haziƙai ba ne, dukansu, kowa ya nufi inda ya ga dama. Kowa yana ta nemar wa kansa riba. 12Sukan ce, “Zo mu samo ruwan inabi, bari mu cika cikinmu da barasa. Gobe ma kamar yau za ta zama, har ma fiye da haka.”

Currently Selected:

Ish 56: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in