“Maganata kamar dusar ƙanƙara take,
Kamar kuma ruwan sama da yake saukowa domin ya jiƙe duniya.
Ba za su kasa sa amfanin gona ya yi girma ba,
Sukan ba da iri domin shukawa, da abinci kuma domin a ci.
To, haka maganar da na faɗa take,
Ba ta kāsa cika abin da na shirya mata,
Za ta yi kowane abin da na aike ta ta yi.