Ish 4
4
1Sa'ad da wannan lokaci ya yi, mata bakwai za su riƙe mutum guda su ce, “Mā iya ciyar da kanmu, mu kuma tufasar da kanmu, amma in ka yarda, bari mu ce kai ne mijinmu, domin kada mu sha kunyar zaman gwagwarci.”
An Ceci Urushalima
2Lokaci na zuwa sa'ad da Ubangiji zai sa kowane tsiro da kowane itacen da take a ƙasar su girma su yi kyau. Dukan jama'ar Isra'ila waɗanda suka ragu za su yi fāriya, su yi murna saboda amfanin da ƙasar take bayarwa. 3Duk wanda aka rage a Urushalima, wanda Ubangiji ya nufa da rayuwa, za a ce da shi mai tsarki. 4Ta wurin ikonsa Ubangiji zai shara'anta al'ummar, ya kuma tsarkake ta, ya wanke laifin Urushalima, har da na jinin da aka zubar a can. 5#Fit 13.21; 24.16 Sa'an nan a kan Dutsen Sihiyona, da a kan dukan waɗanda suka tattaru a can, Ubangiji zai aika da girgije da rana, hayaƙi da hasken harshen wuta kuma da dare. Darajar Ubangiji za ta rufe, ta kuma kiyaye birnin duka. 6Ɗaukakarsa za ta inuwantar da birnin daga zafin rana, ta sa ya zama lafiyayyen wurin da aka kāre daga ruwan sama da hadiri.
Currently Selected:
Ish 4: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979