Ish 5
5
Waƙar Gonar Inabi
1 #
Mat 21.33; Mar 12.1; Luk 20.9 Ku saurara in raira muku wannan waƙa,
Waƙar abokina da gonar inabinsa.
Abokina yana da gonar inabi
A wani tudu mai dausayi.
2Ya kauce ƙasar ya tsintsince duwatsun,
Ya daddasa itatuwan inabi mafi kyau.
Ya gina hasumiya don a yi tsaronsu,
Ya kuma haƙa rami inda za a matse 'ya'yan inabin.
Ya yi ta jira don 'ya'yan inabin su nuna,
Amma ko wannensu tsami take gare shi.
3Saboda haka, abokina ya ce, “Ku jama'ar da yake zaune a Urushalima da Yahuza, ku shara'anta tsakanina da gonar inabina. 4Akwai abin da ban yi mata ba? Me ya sa ta yi 'ya'yan inabi masu tsami, maimakon 'ya'yan inabi masu kyau da nake sa zuciya.
5“Ga abin da zan yi wa gonar inabina. Zan cire shingen da yake kewaye da ita, in rushe bangon da ya kāre ta, in bar namomin jeji su cinye ta, su tattake ta. 6Zan bar ciyayi su rufe ta. Ba zan yi wa kurangar inabin aski ba, ko in yi mata noma, amma zan bar sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa su rufe ta. Har ma zan sa gizagizai su hana ta ruwan sama.”
7Isra'ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna,
Jama'ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa.
Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau,
Amma a maimakon haka sai suka zama masu kisankai!
Ya zaci za su aikata abin da yake daidai,
Amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci!
Mugaye Sun Shiga Uku
8Kun shiga uku! Kuna ƙara wa kanku gidaje da gonaki a kan waɗanda kuke da su a dā. Ba da jimawa ba za a ga ba sauran filin da zai ragu ga kowa, ku kaɗai za ku zauna a ƙasar. 9Na ji Ubangiji Mai Runduna yana cewa, “Duk waɗannan manya manyan gidaje kyawawa za su zama kangwaye. 10Kadada biyar na gonar inabi za ta ba da kwalaba shida kaɗai na ruwan inabi. Garwa ashirin na iri za su ba da tsabar hatsi garwa biyu!”
11Kun shiga uku! Kukan tashi da sassafe ku fara sha, ku yi ta sha har yamma ta yi sosai, ku raba dare kuna buguwa. 12A cikin bukukuwanku kuna kaɗa garaya, da bandiri, da bushe-bushe, da ruwan inabi. Amma ba ku gane da abin da Ubangiji yake yi ba. 13Don haka za a kwashe ku, ku zama 'yan sarƙa, a raba ku da ƙasarku. Yunwa za ta kashe shugabanninku, sauran jama'a kuwa ƙishirwa za ta kashe su. 14Lahira ta ƙosa, ta wage bakinta. Ta lanƙwame manyan mutanen Urushalima da sauran babban taron jama'a masu hayaniya.
15Za a kunyatar da kowa, dukan masu girmankai za a ƙasƙantar da su. 16Amma Ubangiji Mai Runduna yana nuna girmansa ta wurin aikata abin da yake daidai, yana kuma bayyana shi Mai Tsarki ne, ta yadda yake shara'anta jama'arsa. 17A cikin kangwayen birnin, raguna za su ci ciyawa, a nan ne kuma awaki za su sami wurin kiwo.
18Kun shiga uku! Ba ku iya kuɓuta daga zunubanku ba. 19Kukan ce, “Bari Ubangiji ya gaggauta ya aikata abin da ya ce zai yi don mu gani. Bari Allah, Mai Tsarki na Isra'ila, ya i da shirye-shiryensa. Bari mu ga abin da yake nufi.”
20Kun shiga uku! Kun ce mugunta ita ce nagarta, nagarta kuwa mugunta. Kun mai da duhu shi ne haske, haske kuwa duhu. Kun mai da abin da yake mai ɗaci mai zaƙi, mai zaƙi kuwa kun maishe shi mai ɗaci.
21Kun shiga uku! A tsammaninku ku masu hikima ne, masu wayo ƙwarai.
22Kun shiga uku! Jarumawan kwalabar ruwan inabi! Masu ƙarfin zuciya marasa tsoro a gauraya shaye-shaye! 23Amma kukan ƙyale masu laifi waɗanda suka ba ku rashawa, kukan kuwa ƙi yi wa marasa laifi shari'ar gaskiya. 24Don haka, kamar yadda tattaka da busasshiyar ciyawa sukan yanƙwane su ƙone a wuta, saiwoyinku za su ruɓe, furanninku kuma za su bushe. Iska za ta kwashe su, domin kun ƙi abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya koya muku. 25Ubangiji yana fushi da jama'arsa, ya miƙa hannunsa domin ya hukunta su. Duwatsu za su jijjigu, gawawwaki kuwa za a bar su a kan tituna kamar shara. Duk da haka Ubangiji ba zai huce daga fushinsa ba, ba kuwa zai janye hannunsa daga yin hukunci ba.
26Ubangiji ya ba da alama a kirawo al'ummar da take nesa. Ya yi musu fīto su zo daga bangon duniya. Ga shi kuwa sun iso da sauri nan da nan. 27Ko ɗaya ba wanda ya gaji, ba kuwa wanda ya yi tuntuɓe. Ba su yi gyangyaɗi ko barci ba. Ba abin ɗamarar da ya kwance, ba igiyar takalmin da ta tsinke. 28Kibansu masu tsini ne, bakunansu kuwa a shirye suke don yin harbi. Kofaton dawakansu suna da ƙarfi kamar dutsen ƙanƙara, ƙafafun karusansu kamar guguwa ne. 29Sojojinsu na ruri kamar zakunan da suka kashe nama, suna kuwa ɗauke da shi don kada wani ya ƙwace musu.
30Sa'ad da ranar ta yi, za su yi ruri a kan Isra'ila da ƙarfi kamar rurin teku. Ku duba ƙasan nan! Duhu da damuwa! Duhu ya haɗiye hasken.
Currently Selected:
Ish 5: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979