Ish 3
3
Hukuncin Ubangiji a kan Yahuza da Urushalima
1Yanzu fa Ubangiji, Ubangiji Mai Runduna, yana gab da ya kwashe kowane abin da kowane mutum da jama'ar Urushalima da na Yahuza suke dogara da su. Zai kwashe abincinsu da ruwan shansu, 2da jarumawansu, da sojojinsu, da alƙalansu, da annabawansu, da masu yi musu duba, da manyan mutanensu, 3da shugabannin sojojinsu, da na farar hula, da 'yan siyasarsu, da kowane mai aikin sihiri don ya sarrafa abubuwan da yake faruwa. 4Ubangiji zai sa yaran da ba su balaga ba su mallaki jama'ar. 5Za a yi ta cutar juna. Matasa ba za su girmama manyansu ba, talakawa ba za su girmama na gaba da su ba.
6Lokaci yana zuwa sa'ad da mutanen wani dangi za su zaɓi ɗaya daga cikinsu, su ce, “Kai da kake da ɗan abin sawa za ka zama shugabanmu a wannan lokaci na wahala.”
7Amma zai amsa, ya ce, “Ba ni ba dai! Ba zan iya taimakonku ba. Ba ni ma da abinci sam, ko tufafi ma. Kada ku naɗa ni shugabanku!”
8Hakika Urushalima ta shiga uku! Yahuza tana kan fāɗuwa! Duk abin da suke faɗa, da abin da suke yi, na gāba da Ubangiji ne, a fili suke raina Allah, shi kansa. 9Ayyukansu na son zuciya za su zama shaida gāba da su. Suna ta aikata zunubi a fili, kamar yadda mutanen Saduma suka yi. Sun shiga uku, su ne kuwa suka jawo wa kansu.
10Adalai za su yi murna, kome zai tafi musu daidai. Za su ji daɗin abin da suka aikata. 11Amma mugaye sun shiga uku, za a sāka musu bisa ga abin da suka aikata.
12Masu ba da rance da ruwa suna zaluntar jama'ata, masu ba da bashi kuwa suna cutarsu.
Ya jama'ata, shugabanninku a karkace suke bi da ku, saboda haka ba ku san inda za ku nufa ba.
Ubangiji Yana Hukunta Jama'arsa
13Ubangiji a shirye yake ya hurta maganarsa, a shirye yake ya hukunta al'ummai. 14Ubangiji ya kawo dattawa da shugabannin jama'arsa a gaban shari'a. Ga laifin da ya same su da shi, “Kun washe gonakin inabi, kun cika gidajenku da abin da kuka ƙwato daga matalauta. 15Ba ku da izinin da za ku ragargaza jama'ata, ku cuci matalauta, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
Hukunci a kan Matan Urushalima
16Ubangiji ya ce, “Duba irin girmankai da matan Urushalima suke da shi! Suna tafe suna hura hanci, a koyaushe suna ta fara'a irin ta yaudara, suna takawa ɗaya ɗaya a hankali da mundaye a ƙafafunsu, suna cas cas. 17Amma zan hukunta su, in aske kawunansu, in bar su ƙwal.”
18Rana tana zuwa sa'ad da Ubangiji zai raba matan Urushalima da dukan abin da suke taƙama da shi, da kayan adon da suke sawa a ƙafafunsu, da kawunansu, da wuyansu, 19da hannuwansu. Zai raba su da lulluɓinsu, 20da hulunansu. Zai raba su da layun da suke sa wa damatsansu, da kwankwasonsu, 21da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu. 22Ubangiji zai raba su da dukan kyawawan rigunansu na ado, da manyan rigunansu, da mayafansu, da jakunkunansu, 23da rigunansu na yanga, da ƙyallayensu na lilin, da adikai, da gyale masu tsawo waɗanda suke sawa a kawunansu.
24Maimakon su riƙa ƙanshin turare, za su yi wari, a maimakon abin ɗamara, za su yi ɗamara da igiyoyi masu kaushi, a maimakon su kasance da kyakkyawan gashi, za su zama masu sanƙo, a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki, kyansu zai zama abin kunya!
25Jama'ar garin, i, har da ƙarfafan mutane, za a kashe su a yaƙi. 26Ƙofofin birnin za su yi makoki, su yi kuka.
Za a kamanta birnin da matar da take zaune a ƙasa tsirara.
Currently Selected:
Ish 3: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979