YouVersion Logo
Search Icon

Ish 33

33
Ubangiji Zai Kawo Ceto
1Magabtanmu sun shiga uku! Sun yi fashi sun ci amana, ko da yake ba wanda ya yi musu fashi ko cin amana. Amma lokacinsu na fashi da na cin amana zai ƙare, su ne kuma za a yi wa fashi da cin amana.
2Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai. Muna sa zuciyarmu gare ka. Ka dinga kiyaye mu yau da gobe, ka kuma cece mu a lokatan wahala. 3Lokacin da kake yaƙi dominmu, al'ummai sukan gudu daga bakin dāga. 4Akan tsirga a bisa abubuwan da suke da su, a kwashe su ganima.
5Ubangiji da girma yake! Yana mulki a kan kome. Zai cika Urushalima da adalci da mutunci, 6zai kuma sa aminci cikin al'ummar. A koyaushe yakan kiyaye jama'arsa ya kuma ba su hikima da sani. Dukiyarsu mafi girma ita ce tsoron Ubangiji.
7Mutane masu jaruntaka suna kira don a taimake su! Jakadu waɗanda suke ƙoƙarin kawo salama suna kuka mai zafi. 8Manyan karauku suna da hatsari har ba mai iya binsu. Aka keta yarjejeniya, aka ta da sharuɗa. Ba a kuma ganin girman kowa. 9Ƙasar na zaman banza, an gudu an bar ta. Jejin Lebanon ya bushe, kwarin Sharon mai dausayi ya zama kamar hamada, a Bashan kuma da a kan Dutsen Karmel sai ganyaye suke karkaɗewa daga itatuwa.
10Ubangiji ya ce wa al'ummai, “Yanzu zan tashi! Zan nuna irin ikon da nake da shi. 11Kuka yi shirye-shiryen banza, kowane abu da kuke yi kuma ba shi da amfani. Kuna hallakar da kanku! 12Za ku marmashe kamar duwatsun da aka ƙona don a yi farar ƙasa, kamar ƙayayuwan da aka ƙone suka zama toka. 13Bari kowa da yake kusa da na nesa ya ji abin da na yi, ya kuma san ikona.”
14Jama'ar Sihiyona cike da zunubi suke, suna ta rawar jiki don tsoro. Suka ce, “Hukuncin Allah kamar wuta ce mai ci har abada. Akwai wani daga cikinmu da zai iya tsira daga irin wannan wuta?” 15Kuna iya tsira idan kuna faɗar gaskiya kuna kuma yin abin da yake daidai. Kada ku gwada ikonku don ku cuci talakawa, kada kuwa ku karɓi rashawa. Kada ku haɗa kai da masu shiri su yi kisankai, ko su aikata waɗansu mugayen abubuwa. 16Sa'an nan za ku yi nasara, ku kuma zauna lafiya kamar kuna cikin kagara mai ƙarfi. Za ku sami abincin da za ku ci da ruwan da za ku sha.
Gaba Mai Daraja
17Wata rana za ku ga sarki mai ɗaukaka yana mulki a dukan ƙasar da take shimfiɗe zuwa kowace kusurwa. 18Tsoronku na dā game da baƙi masu tara haraji, magewaya, zai ƙare. 19Ba za ku ƙara ganin baƙin nan masu girmankai, masu magana da harshen da ba ku fahimta ba! 20Ku duba Sihiyona, birni inda muke idodinmu. Ku duba Urushalima! Za ta zama wurin zama mai lafiya! Za ta zama kamar alfarwar da ba ta taɓa gusawa ba, wadda ba a taɓa tumɓuke turakunta ba, igiyoyinta kuma ba su taɓa tsinkewa ba. 21Ubangiji zai nuna mana ɗaukakarsa. Za mu zauna a gefen koguna da rafuffuka masu faɗi, amma ba kuwa jirgin ruwan abokan gāba da zai bi ta cikinsu. 22-23Dukan kayayyakin waɗannan jiragen ruwa ba su da amfani, tafiyarsu ba za ta yi nisa ba! Za a kwashe dukan dukiyar sojojin abokan gāba. Za ta yi yawa har sauran jama'a za su sami rabonsu. Ubangiji kansa shi zai zama sarkinmu, zai mallake mu, ya kiyaye mu. 24Ba wanda zai zauna a ƙasarmu har ya ƙara yin kukan yana ciwo, za a kuma gafarta dukan zunubai.

Currently Selected:

Ish 33: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in