Ish 34
34
Ubangiji Zai Hukunta Edom
1Ku zo, ku jama'ar dukan al'ummai! Ku tattaru ku kasa kunne. Bari dukan duniya, da kowane mai zama cikinta, ya zo nan ya kasa kunne. 2Ubangiji yana fushi da al'ummai duka, da kuma dukan sojojinsu. Ya zartar musu da hukuncin hallaka. 3Ba za a binne gawawwakinsu ba, amma za a bar su can, su ruɓe, su yi ɗoyi, duwatsu kuma za su yi ja wur da jini. 4#Mat 24.29; Mar 13.25; Luk 21.26; W.Yah 6.13,14 Za a murtsuke rana, da wata, da taurari su zama ƙura. Sararin sama zai shuɗe kamar yadda ake naɗe littafi, taurari kuma su faɗo kamar yadda ganyaye suke karkaɗewa daga itacen inabi ko na ɓaure.
5 #
Ish 63.1-6; Irm 49.7-22; Eze 25.12-14; 35.1-15; Amos 1.11,12; Oba 1.1-14; Mal 1.2-5 Ubangiji ya shirya takobinsa a can Sama, yanzu kuwa zai buga Edom, wato mutanen can da ya zartar musu da hukuncin hallaka. 6Jininsu da kitsensu za su rufe takobinsa, kamar jini da kitsen raguna, da na awaki, da aka miƙa hadaya. Ubangiji zai yi wannan hadaya a birnin Bozara, zai sa wannan ya zama babban kisa a ƙasar Edom. 7Mutane za su fāɗi kamar bijiman jeji da 'yan bijimai, ƙasar za ta yi ja wur da jini, kitse kuma zai rufe ta. 8Wannan shi ne lokacin da Ubangiji zai kuɓutar da Sihiyona, ya kuma ɗauki fansa a kan abokan gābanta.
9Kogunan Edom za su zama kalo, wato kwalta, ƙasar za ta zama kibritu, wato farar wuta. Dukan ƙasar za ta ƙone kamar kalo. 10#W.Yah 14.11; 19.3 Za ta yi ta ci dare da rana, hayaƙi zai yi ta tashi sama har abada. Ƙasar za ta zama marar amfani shekara da shekaru, ba wanda zai iya ƙara bi ta cikinta. 11Mujiyoyi da hankaki su ne za su gāji ƙasar. Ubangiji zai maishe ta marar amfani, kamar yadda take tun kafin halitta. 12Ba sarkin da zai yi mulkin ƙasar, dukan shugabanni kuma za su ƙare. 13Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su tsiro su yi girma a cikin dukan fādodi da garuruwa masu garuka, diloli da mujiyoyi za su zauna a cikinsu. 14Namomin jeji za su yi ta kaiwa da komowa a can suna kiran juna. Mugun naman jeji zai je can ya nemi wurin hutawa. 15Mujiyoyi za su yi sheƙarsu a can, su nasa ƙwayaye, su ƙyanƙyashe 'ya'yansu, su kuma lura da su a can. Ungulai za su tattaru a can a kai a kai.
16Bincika cikin Littafin Ubangiji ka karanta abin da yake faɗa. Ba ko ɗaya cikin halittattun nan da zai ɓata ba, ba kuwa wanda zai rasa ɗan'uwansa. Ubangiji ne ya umarta ya zama haka, shi kansa zai kawo su tare. 17Ubangiji ne zai rarraba musu ƙasar, ya kuma ba ko wannensu nasa rabo. Za su zauna a ƙasar shekara da shekaru, za ta kuwa zama tasu har abada.
Currently Selected:
Ish 34: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979