YouVersion Logo
Search Icon

Ish 32

32
Sarki Mai Adalci
1Wata rana za a yi wani sarki mai adalci, da kuma shugabannin ƙasa waɗanda za su yi mulki da gaskiya. 2Ko wannensu zai zama kamar wurin fakewa daga iska da kuma wurin ɓuya saboda hadiri, za su zama kamar rafuffukan da suke gudu cikin hamada, kamar inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa. 3Idanunsu da kunnuwansu za su kasance a buɗe domin sauraron jama'a. 4Za su zama masu haƙuri sosai, za su yi kome da haziƙanci, za su kuma faɗi abin da suke nufi. 5Ba wanda zai girmama wawayen mutane, ko kuma ya ce da mazambata suna da aminci. 6Dakiki yakan yi maganar wauta ya kuma yi tunanin mugayen ayyukan da zai aikata. Abin da dakiki yakan aikata da abin da yakan faɗa, duk ɓatanci ne ga Allah, bai kuwa taɓa ciyar da masu jin yunwa ba, ko ya ba masu jin ƙishi ruwa su sha. 7Mugu ne shi, yana kuwa yin mugayen abubuwa, yakan yi shiri don ya lalatar da matalauta da ƙarya, ya kuma hana su samun hakkinsu. 8Amma mutum mai aminci yakan yi aikin aminci ya kuwa tsaya da ƙarfi a kan abin da yake daidai.
An Yi wa Matan Urushalima Faɗaka
9Ku matan da kuke zaman jin daɗi, ba ku da damuwar kome, ku kasa kunne ga abin da nake faɗa. 10Zai yiwu ku wadatu yanzu, amma baɗi war haka za ku fid da zuciya, gama ba inabin da za ku tattara. 11Kuna ta zaman jin daɗi, ba abin da yake damunku, amma yanzu ku yi rawar jiki don tsoro! Ku tuɓe tufafinku ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku. 12Ku bugi ƙirjinku don baƙin ciki, gama an lalatar da gonaki masu dausayi da kuma gonakin inabi, 13ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya ne suke girma a ƙasar jama'ata. Ku yi kuka domin dukan gidajen da mutane suke murna a cikinsu dā, domin kuma birnin da yake cike da jin daɗi a dā. 14Har ma za a bar fādar, babban birnin sarauta kuma za a gudu a bar shi gaba ɗaya. Gidaje kuma da kagaran da take tsaronsu za su zama rusassu har abada. A can jakunan jeji za su yi ta zarya, tumaki kuma za su sami wurin kiwo.
15Amma Allah zai ƙara aiko mana da Ruhunsa. Ƙasar da ta zama marar amfani za ta komo mai dausayi, gonaki kuma za su ba da amfani mai yawa. 16A ko'ina a ƙasar za a aikata adalci da gaskiya. 17Gama kowa zai yi abin da yake daidai, za a sami salama da zaman lafiya har abada. 18Gidajen jama'ar Allah za su zama da salama da zaman lafiya, ba abin da zai dame su. 19(Amma ƙanƙara za ta faɗo a jeji, za a kuma rurrushe birni.) 20Kowa zai yi murna da ruwan sama mai yawa domin amfanin gona, da kuma lafiyayyiyar makiyaya domin jakuna da shanu.

Currently Selected:

Ish 32: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in