YouVersion Logo
Search Icon

Ish 14

14
Takama Gāba da Sarkin Babila
1Ubangiji zai sāke yi wa jama'arsa Isra'ila jinƙai, ya zaɓe su su zama nasa. Zai sāke sa su zauna a ƙasarsu, baƙi ma za su zo su zauna tare da su. 2Al'ummai da yawa za su taimaki jama'ar Isra'ila su koma ƙasarsu wadda Ubangiji ya ba su. A can sauran al'umma za su yi wa Isra'ila hidima kamar bayi. Waɗanda suka kama Isra'ilawa a dā yanzu Isra'ilawa za su kama su. Jama'ar Isra'ila za ta mallaki waɗanda suka taɓa zaluntarsu.
3Ubangiji Allah kuwa zai sawwaƙe wa jama'ar Isra'ila azaba da wahala da suke sha, daga kuma aikin da aka tilasta su su yi. 4Sa'ad da ya aikata wannan za su yi wa Sarkin Babila ba'a.
Za su ce, “Mugun sarkin ya fāɗi, ba zai ƙara zaluntar kowa ba! 5Ubangiji ya ƙare mulkin mugun, 6wanda yake zaluntar jama'a a husace, bai taɓa daina tsananta wa al'ummai ba, wanda ya ci da yaƙi. 7Yanzu magana ta ƙare, duniya duka tana jin daɗin hutawa da salama. Kowa na ta raira waƙar murna. 8Itatuwan fir da itatuwan al'ul na Lebanon suna murna da faɗuwar sarkin! Ba wanda zai tasar musu da sara!
9“Lahira tana shirye-shiryen yi wa Sarkin Babila maraba. Fatalwan waɗanda suka yi iko a duniya suna kaiwa suna komowa a hargitse. Fatalwan sarakuna suna tashi daga gadajen sarautarsu. 10Dukansu suka yi kira gare shi, suka ce, ‘Ashe, kai ma rarrauna ne kamarmu! Ka zama ɗaya daga cikinmu. 11Dā ana ɗaukaka ka da kaɗe-kaɗen garaya, amma yanzu ga ka a lahira! Kana kwance a kan tsutsotsi. Kana rufe da tsutsotsi!’ ”
12 # W.Yah 8.10; 9.1 Ya Sarkin Babila, kai da kake tauraron asubahi mai haske, ka fāɗo daga sama. A dā ka ci al'ummai da yaƙi amma yanzu an fyaɗa ka ƙasa. 13#Mat 11.23; Luk 10.15 Ka yi niyyar hawan sama, ka sa gadon sarautarka a kan taurari mafi nisa. Ka zaci za ka zauna kamar sarki a kan dutsen nan na arewa, inda alloli suke tattare. 14Kai ka ce za ka hau can bisa kan taurari, ka zama kamar Mai Iko Dukka. 15Amma a maimakon haka an saukar da kai a sashe mafi zurfi a lahira.
16Matattu za su zura maka ido su yi mamaki. Za su yi tambaya su ce, “Ashe, ba wannan mutum ba ne ya girgiza duniya, ya sa mulkoki suka jijjigu? 17Wannan shi ne wanda ya hallaka birane, ya mai da duniya hamada, wanda bai taɓa sakin ɗaurarru ko ya bar su su koma gida ba?” 18Dukan sarakunan duniya suna kwance a cikin manya manyan kaburburansu, 19amma kai ba ka sami kabari ba, jefar da gawarka aka yi don ta ruɓe. Aka hautsuna gawarka da gawawwakin mayaƙan da aka kashe cikin yaƙi. Tare da su aka jefa ka gangaren dutse, aka tattake. 20Ba za a binne ka kamar sauran sarakuna ba, saboda ka lalata da ƙasarka, ka karkashe mutanenka. Daga cikin mugayen iyalinka ba wanda zai ragu. 21A fara yanyanka su! 'Ya'ya maza na sarkin nan za su mutu saboda zunuban kakanninsu. Daga cikinsu ba wanda zai taɓa mallakar duniya, ko ya cika ta da birane.
Allah Zai Hallaka Babila
22Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan fāɗa wa Babila da yaƙi, in lalata ta, ba abin da zan bari, ko yara, ba wanda zai ragu. Ni, Ubangiji, na faɗi wannan. 23Zan su Babila ta zama fadama, mujiyoyi za su zauna a can. Zan kuwa share Babila da tsintsiyar da za ta share kome. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗa.”
Allah Zai Hallaka Assuriya
24 # Ish 10.5-34; Nah 1.1—3.19; Zaf 2.13-15 Ubangiji Mai Runduna ya rantse, ya ce, “Abin da na riga na shirya, haka zai faru. Abin da na yi niyyar yi, za a yi. 25Zan hallaka Assuriyawa a ƙasata ta Isra'ila, in tattake su a kan duwatsuna. Zan 'yantar da jama'ata daga karkiyar Assuriyawa, daga nauyin da suka tilasta musu su ɗauka. 26Abin da na shirya zan yi wa duniya, shi ne in miƙa hannuna domin in hukunta wa al'ummai.” 27Ubangiji Mai Runduna ne ya ƙudura ya yi wannan, ya miƙa dantsensa don ya yi hukunci, ba kuwa mai iya hana shi.
Annabci a kan Filistiya
28 # 2Sar 16.20; 2Tar 28.27 Wannan shi ne jawabin da aka yi shelarsa a shekarar da sarki Ahaz ya rasu.
29 # Irm 47.1-7; Eze 25.15-17; Yow 3.4-8; Amos 1.6-8; Zaf 2.4-7; Zak 9.5-7 Ku mutanen Filistiya, sandan da ake dūkanku da shi ya karye, amma kada wannan ya zamar muku dalilin murna. Gama idan wani maciji ya mutu, wani mafi mugunta zai maye gurbinsa. Ƙwan maciji yake ƙyanƙyashe maciji mai tashi sama! 30Ubangiji zai zama makiyayin jama'arsa wadda take talauce, zai kuma sa su zauna lafiya. Amma ku Filistiyawa, zai aukar muku da matsananciyar yunwa, wadda ba za ta bar ko ɗayanku da rai ba.
31Ku yi kururuwa, ku yi kuka na neman taimako, dukanku biranen Filistiya! Ku razana dukanku! Ƙurar da ta murtuke tana zuwa daga arewa, mayaƙa ne, ba kuwa matsorata a cikinsu.
32Ƙaƙa za mu amsa wa manzannin da suka zo gare mu daga Filistiya? Za mu faɗa musu, cewa Ubangiji ya tabbatar da Sihiyona, jama'arsa da suke shan wahala kuwa za su sami zaman lafiya a can.

Currently Selected:

Ish 14: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in