Ish 15
15
Annabci a kan Mowab
1 #
Ish 25.10-12; Irm 48.1-47; Eze 25.8-11; Amos 2.1-3; Zaf 2.8-11 Wannan shi ne jawabi a kan Mowab.
Biranen Ar da Kir, an hallaka su dare ɗaya, ƙasar ta yi tsit, ba kowa. 2Mutanen Dibon sun hau kan tuddai don su yi kuka a matsafarsu. Mutanen Mowab suna kuka da baƙin ciki saboda biranen Nebo da Medeba, sun aske kawunansu da gyammansu saboda baƙin ciki. 3Mutane a tituna sun sa tsummoki a jikinsu, suka taru a filayen taruwa na birni da a kan rufin ɗakuna, sai makoki suke suna ta kuka. 4Mutanen Heshbon da na Eleyale suka yi kuka da ƙarfi, har ana iya jin kukansu daga Yahaza. Har mayaƙa ma sun yi rawar jiki, zuciyarsu ta karai. 5Zuciyata ta yi kuka ainun saboda Mowab! Mutane sun gudu zuwa cikin garin Zowar. Waɗansu sun haura zuwa Luhit, suna tafe suna kuka, waɗansu sun tsere zuwa Horonayim, suna hargowa saboda baƙin ciki. 6Rafin Nimra ya ƙafe, ciyawar da take gefensa ta bushe, ba sauran wani ɗanyen abu. 7Mutane sun haye kwarin Larabawa, suna ƙoƙari su tsere da dukan abin da suka mallaka. 8A ko'ina a kan iyakokin Mowab, sai ƙugin kukansu ake ji. Ana kuwa ji daga garuruwan Eglayim da Biyer-elim. 9A garin Dibon, kogin ya yi ja wur da jini, Allah kuwa ya tanada wa mutanen wurin abin da ya fi wannan muni. Hakika za a yi wa duk wanda ya ragu a Mowab mummunan kisa.
Currently Selected:
Ish 15: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979