YouVersion Logo
Search Icon

Yush 2

2
Ubangiji Yana Ƙaunar Mutanensa Marasa Aminci
1“Ka ce wa 'yan'uwanka maza, ‘Ku mutanena ne,’ ka kuma ce wa 'yar'uwarka, ‘Kin sami jinƙai!’
2“Ku roƙi uwarku,
Gama ita ba matata ba ce,
Ni kuma ba mijinta ba ne.
Ku roƙe ta ta daina karuwancinta,
Ta rabu da masu rungumar mamanta.
3In ba haka ba, sai in yi mata tsiraici,
In bar ta kamar ran da aka haife ta.
In maishe ta kamar jeji,
In bar ta kamar busasshiyar ƙasa,
In kashe ta da ƙishi.
4Ba zan yi wa 'ya'yanta jinƙai ba,
Domin su 'ya'yan karuwanci ne
5Gama uwarsu ta yi karuwanci.
Ita wadda ta haife su ta yi abin kunya.
Gama ta ce, ‘Zan bi samarina
Waɗanda suke ba ni ci da sha,
Da ulu, da lilin, da mai, da ruwan inabi.’
6“Don haka zan shinge hanyarta da ƙaya,
Zan gina mata garu don kada ta sami hanyar fita.
7Za ta bi samarinta, amma ba za ta tarar da su ba.
Za ta neme su, amma ba za ta same su ba.
Sa'an nan za ta ce, ‘Zan koma wurin mijina na fari,
Gama zamana na dā ya fi na yanzu!’
8“Amma ba ta sani ni nake ba ta hatsi, da ruwan inabi, da mai,
Da azurfa, da zinariya da yawa
Waɗanda suka bauta wa gunkin nan Ba'al da su ba.
9Don haka zan hana mata hatsi a kakarsa,
Da ruwan inabi a kakarsa, da kuma ulu da lilin
Waɗanda suka zama abin rufe tsiraicinta.
10Yanzu zan buɗe tsiraicinta
A idon samarinta,
Ba kuwa wanda zai cece ta daga hannuna.
11Zan sa ta daina farin cikinta,
Da idodinta, da kiyaye lokatan amaryar wata,
Da hutawar ranar Asabar,
Da ƙayyadaddun idodinta.
12Zan ɓata inabinta da itatuwan ɓaure
Waɗanda take cewa, ‘Waɗannan su ne hakkina
Wanda samarina suka ba ni.’
Zan sa su zama kurmi,
Namomin jeji su cinye su.
13Zan hukunta ta saboda kwanakin idodin gunkin nan Ba'al.
A kwanakin nan takan ƙona musu turare,
Ta yi ado da zobe da lu'ulu'ai,
Ta bi samarinta, amma ta manta da ni.”
In ji Ubangiji.
14“Don haka, ga shi, zan rarrashe ta,
In kai ta cikin jeji,
In ba ta magana.
15 # Josh 7.24-26 Can zan ba ta gonar inabi,
In mai da kwarin Akor, wato wahala, ƙofar bege.
A can za ta amsa mini kamar a kwanakin ƙuruciyarta,
Kamar lokacin da ta fito daga ƙasar Masar.
16Ni Ubangiji na ce, a waccan rana
Za ta ce da ni,
‘Mijina,’ ba za ta ƙara ce da ni Ba'al ba.
17Zan kawar da sunayen Ba'al daga bakinta.
Ba za a ƙara kiransu da sunayensu ba.
18“A waccan rana zan yi alkawari
Da namomin jeji, da tsuntsaye,
Da abubuwa masu rarrafe saboda Isra'ila.
Zan kuma kakkarya baka da takobi,
In kuma sa yaƙi ya ƙare a ƙasar,
Sa'an nan za su yi zamansu lami lafiya.
19Zan ɗaura auren da yake cikin adalci,
Da bisa kan ka'ida, da ƙauna.
20Zan ɗaura auren da yake cikin aminci,
Za ki kuwa sani, ni ne Ubangiji.
21“A waccan rana, zan amsa wa sammai,
Su kuma za su amsa wa ƙasa.
22Ƙasa kuma za ta amsa wa hatsi, da ruwan inabi, da mai,
Su ma za su amsa wa Yezreyel.
23 # Rom 9.25; 1Bit 2.10 Zan dasa ta a ƙasa domin kaina.
Zan kuma yi wa ‘Ba-jinƙai,’ jinƙai,
In kuma ce wa ‘Ba-mutanena ba,’ ‘Mutanena!’
Su ma za su ce, ‘Kai ne Allahna!’ ”

Currently Selected:

Yush 2: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in