YouVersion Logo
Search Icon

Yush 3

3
Yusha'u da Karuwa
1Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka sāke tafiya, ka ƙaunaci karuwa wadda take tare da kwartonta. Ka ƙaunace ta kamar yadda ni Ubangiji nake ƙaunar mutanen Isra'ila, ko da yake suna bin gumaka, suna ƙaunar wainar zabibi da aka miƙa wa gumaka.”
2Sai na ba da sadakinta a bakin tsabar azurfa goma sha biyar, da buhu biyu na sha'ir. 3Sa'an nan na ce mata, “Ki keɓe kanki kwanaki da yawa domina, kada ki yi kwartanci, ki kwana da wani, ni kuma ba zan shiga wurinki ba.” 4Gama mutanen Isra'ila za su zauna kwanaki da yawa ba sarki, ba shugaba, ba sadaka, ba al'amudi, ba falmaran, ba kan gida. 5Bayan wannan mutanen Isra'ila za su komo su nemi Ubangiji Allahnsu, da Dawuda, sarkinsu. Da tsoro za su komo zuwa wurin Ubangiji domin alheransa a kwanaki na ƙarshe.

Currently Selected:

Yush 3: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in