Yush 1
1
Matar Yusha'u wadda Ta Ci Amanarsa da 'Ya'yanta
1 #
2Sar 15.1-7; 2Tar 26.1-23;
2Sar 15.32-38; 2Tar 27.1-8;
2Sar 16.1-20; 2Tar 28.1-27;
2Sar 18.1—20.21; 2Tar 29.1—32.33;
2Sar 14.23-29
Ubangiji kuwa ya yi magana da Yusha'u ɗan Beyeri a zamanin mulkin Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, sarakunan Yahuza, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yehowash, Sarkin Isra'ila.
2Sa'ad da Ubangiji ya fara yin magana da Yusha'u ya ce masa, “Tafi ka auro karuwa, ka haifi 'ya'yan karuwanci, gama ƙasar tana yin fasikanci sosai, wato ta bar bin Ubangiji.”
3Sai ya tafi ya auri Gomer, 'yar Diblayim. Ta yi ciki, ta haifi masa ɗa namiji. 4#2Sar 10.11 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka raɗa masa suna, Yezreyel, gama ba da daɗewa ba zan ziyarci gidan Yehu da hukunci saboda jinin da ya zubar a Yezreyel. Zan sa mulkin Isra'ila ya ƙare. 5A wannan rana zan karya bakan Isra'ila a kwarin Yezreyel.”
6Gomer ta kuma ɗauki ciki, ta haifi 'ya mace. Ubangiji kuma ya ce wa Yusha'u, “Ka raɗa mata suna Bajinƙai, gama ba zan ƙara yi wa jama'ar Isra'ila jinƙai ba, har da zan gafarta mata. 7Amma zan yi wa mutanen Yahuza jinƙai. Ni kaina zan cece su ba da baka ba, ba kuwa da takobi, ko da yaƙi, ka da dawakai, ko da sojojin dawakai ba.”
8Sa'ad da ta yaye Ba-jinƙai, ta sāke ɗaukar ciki, ta haifi ɗa namiji. 9Ubangiji kuma ya ce masa, “Ka raɗa masa suna, Ba-mutanena-ba-ne, gama ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne.
10 #
Rom 9.26
“Duk da haka yawan mutanen Isra'ila
Zai zama kamar yashi a bakin teku,
Wanda ba za a iya aunawa ko ƙidayawa ba.
Maimakon kuma a ce, ‘Ku ba mutanena ba ne,’
Za a ce, ‘Ku mutanen Allah ne mai rai.’
11Mutanen Yahuza da mutanen Isra'ila za su haɗu su zama ɗaya,
Za su zaɓa wa kansu shugaba ɗaya.
Za su shugabanci ƙasar
Gama ranar Yezreyel babba ce.”
Currently Selected:
Yush 1: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979