YouVersion Logo
Search Icon

Eze 47

47
Kogin da Yake Malalowa daga Haikali
1 # Zak 14.8; Yah 7.38; W.Yah 22.1 Ya komo da ni zuwa ƙofar Haikalin, sai ga ruwa yana bulbulowa daga ƙarƙashin bakin ƙofar Haikalin a wajen gabas, gama Haikalin na fuskantar gabas. Ruwan kuwa yana gangarowa daga gefen kudancin bakin ƙofar Haikalin, a kudancin bagaden. 2Sai ya fito da ni ta hanyar ƙofar arewa, ya kewaya da ni zuwa ƙofar waje wadda take fuskantar gabas. Ruwan kuwa yana gangarowa kaɗan kaɗan daga wajen kudu. 3Mutumin ya nufi wajen gabas da ma'auni a hannunsa, ya auna kamu dubu, sa'an nan ya sa ni in haye ruwan. Zurfin ruwan ya kama ni idon ƙafa. 4Sai kuma ya auna kamu dubu, ya sa ni in haye ruwan. Zurfin ruwan kuwa ya kama ni gwiwa. Sai ya sāke auna kamu dubu, ya sa in haye ruwan, sai zurfin ruwan ya kai ga kama ni gindi. 5Ya sāke auna kamu dubu kuma, sai ruwan ya zama kogi har ban iya in haye ba, gama ruwan ya hau, ya zama da zurfin da ya isa ninƙaya. Ya zama kogin da ba za a iya hayewa ba. 6Sai ya tambaye ni, ya ce. “Ɗan mutum, ka ga wannan?”
Sa'an nan ya komo da ni zuwa gāɓar kogin. 7Sa'ad da nake tafiya, sai na ga itatuwa da yawa a kowace gāɓar kogin. 8Ya kuma ce mini, “Wannan ruwa yana gangarowa zuwa wajen gabas har zuwa cikin Araba. Zai shiga ruwan teku marar gudu, ruwan tekun kuwa zai zama ruwan daɗi. 9Kowace halitta mai rai da take cikin wannan ruwa za ta rayu. Za a sami kifaye da yawa a ciki, domin wannan ruwa zai kai wurin ruwan tekun, zai kuwa zama ruwan daɗi. Duk inda ruwan nan ya tafi kowane abu zai rayu. 10Masunta za su tsaya a gāɓar tekun daga En-gedi zuwa En-eglayim. Gāɓar teku za ta zama wurin shanya taruna. Za a sami kifaye iri iri a cikinta kamar kifaye na Bahar Rum. 11Amma ruwan fadamunsa ba zai yi daɗi ba, za a bar shi a gishirinsa. 12#W.Yah 22.2 A kowace gāɓar kogin, itatuwa iri iri na abinci za su yi girma. Ganyayensu ba za su bushe ba, itatuwan kuma ba za su fasa yin 'ya'ya ba, amma su za su yi ta bayarwa a kowane wata, gama ruwansu yana malalowa daga Haikalin. 'Ya'yansu abinci ne, ganyayensu kuwa magani ne.”
Iyakar Ƙasar
13Ubangiji Allah ya ce, “Waɗannan su ne kan iyaka da za su raba ƙasar gādo ga kabilan Isra'ila goma sha biyu. Yusufu zai sami rabo biyu. 14Za ku raba daidai, gama na rantse zan ba kakanninku wannan ƙasa, za ta kuwa zama gādonku.
15“A wajen arewa, iyakar za ta kama daga Bahar Rum, ta bi ta hanyar Hetlon zuwa Zedad, 16da Hamat, da Berota, da Sibrayim, wadda take a iyakar tsakanin Dimashƙu da Hamat, har zuwa Hazer-hattikon wadda take iyakar Hauran. 17Iyakar za ta bi daga teku zuwa Hazar-enan wadda take iyakar Dimashƙu. Iyakar Hamat tana wajen arewa. Wannan ita ce iyakar a wajen arewa.
18“A wajen gabas, iyakar za ta kama daga Hazar-enan tsakanin Hauran da Dimashƙu, ta bi ta Urdun tsakanin Gileyad da ƙasar Isra'ila zuwa tekun gabas har zuwa Tamar. Wannan ita ce iyakar a wajen gabas.
19“A wajen kudu, iyakar za ta kama daga Tamar har zuwa ruwan Meribakadesh, ta bi ta rafin Masar zuwa Bahar Rum. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.
20“A wajen yamma, Bahar Rum shi ne iyakar zuwa ƙofar Hamat. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.
21“Za ku kuwa raba ƙasar a tsakaninku bisa ga kabilan Isra'ila. 22Za ku raba ƙasar gādo a tsakaninku da baƙin da suke zaune tare da ku, waɗanda suka haifi 'ya'ya a cikinku. Za su zama kamar 'ya'yan Isra'ila haifaffu na gida. Za a ba su gādo tare da kabilan Isra'ila, 23a cikin kabilar da baƙon yake zaune, nan ne za ku ba shi nasa gādo, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Currently Selected:

Eze 47: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in